Eze 46
46
Sarki da Hidimomin Idodi
1“Ni Ubangiji Allah na ce za a rufe ƙofar fili ta can ciki wadda take fuskantar gabas dukan ranaku shida na aiki, amma za a buɗe ta a ranar Asabar da a amaryar wata. 2Sarki zai shiga ta ƙofar shirayi daga waje, sa'an nan ya tsaya kusa da ginshiƙin ƙofar. Sai firistoci su miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayunsa na salama, shi kuwa ya yi sujada s bakin ƙofar, sa'an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da maraice. 3Jama'ar ƙasar za su yi wa Ubangiji sujada a bakin wannan ƙofa a ranakun Asabar da a amaryar wata. 4Hadaya ta ƙonawa da sarki zai miƙa wa Ubangiji a ranar Asabar 'yan raguna shida ne da rago ɗaya marasa lahani. 5Gārin hadaya da za a yi tare da rago wajen garwa guda ne. Wanda za a yi tare da 'yan raguna kuwa zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da mai wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta gari. 6A amaryar wata kuwa zai miƙa bijimi, da 'yan raguna shida, da rago, dukansu marasa lahani. 7Gārin hadayar da za a yi tare da bijimin wajen garwa guda ne, haka kuma gari na wadda za a yi tare da ragon, da gari na wadda za a yi tare da 'yan raguna kuma, zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da man zaitun wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta garin. 8Sa'ad da sarki zai shiga, sai ya shiga ta ƙofar shirayin, ya kuma fita ta nan.
9“Sa'ad da jama'ar ƙasar sun zo yi wa Ubangiji sujada a lokatan ƙayyadaddun idodi, wanda ya shiga ta ƙofar arewa, sai ya fita ta ƙofar kudu. Wanda kuma ya shiga ta ƙofar kudu, sai ya fita ta ƙofar arewa. Kada kowa ya fita ta ƙofar da ya shiga, amma sai kowa ya fita ta akasin ƙofar da ya shiga. 10Sa'ad da suka shiga, sai sarki ya shiga tare da su, sa'ad da suka fita kuma, sai ya fita. 11A lokacin idodi da ƙayyadaddun lokatai, gārin hadayar da za a yi tare da bijimi wajen garwa guda ne, haka kuma na wadda za a yi tare da ragon, na wadda za a yi tare da 'yan ragunan kuwa, sai mutum ya kawo gwargwadon ƙarfinsa. A kuma kawo wajen kwalaba shida na man zaitun domin kowace garwa ta gari.
12“Sa'ad da sarki ya kawo hadayar ƙonawa ko hadayar salama ta yardar rai ga Ubangiji, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai kuwa miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko ta salama kamar yadda yakan yi a ranar Asabar. Bayan da ya fita, sai a rufe ƙofa.
13“Kowace safiya za a yi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji da ɗan rago bana ɗaya marar lahani. 14Tare da hadaya ta ƙonawa, za a ba da wajen ɗaya bisa shida na garwar gari, da kwalaba biyu na man zaitun don cuɗa gari, domin a yi hadaya ga Ubangiji. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa ta yau da kullum. 15Za a ba da ɗan rago, da gari, da mai, kowace safiya domin yin hadaya ta ƙonawa.
16“Ni Ubangiji Allah na ce, idan sarki ya yi wa wani daga cikin 'ya'yansa kyauta daga cikin gādonsa, sai kyautar ta zama ta 'ya'yansa, dukiyarsu ce ta gādo. 17#L.Fir 25.10 Amma idan sarki ya yi wa wani daga cikin barorinsa kyauta daga cikin gādonsa, kyautar za ta zama tasa har shekarar 'yantarwa, sa'an nan kyautar za ta koma a hannun sarki. 'Ya'yansa maza ne kaɗai za su riƙe kyauta daga cikin gādonsa din din din. 18Kada sarki ya ƙwace rabon gādon jama'a, ya hana musu. Sai ya ba 'ya'yansa maza rabon gādo daga cikin abin da yake nasa, amma kada ya ƙwace wa jama'ata abin da suka mallaka har su warwatse.”
19Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar da take gefen ƙofa mai fuskantar arewa, wajen jerin tsarkakakkun ɗakuna na firistoci, waɗanda suke fuskantar arewa. Na kuma ga wani wuri daga can ƙurewar yamma. 20Sai ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya domin laifi, da hadaya domin zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gāri, domin kada su kai su a filin waje, su sa wa mutane tsarki.”
21Ya kuma kai ni a farfajiyar waje, ya bi da ni zuwa kusurwa huɗu na farfajiya. Akwai ɗan fili a kowace kusurwa. 22Girman kowane ɗan fili tsawonsa kamu arba'in ne, faɗin kuma kamu talatin. 23A cikin kowane ɗan fili na kusurwa huɗu ɗin akwai jerin duwatsu. Aka gina murhu ƙarƙashin jerin duwatsun. 24Sa'an nan ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a Haikali za su dafa hadayun da jama'a suka kawo.”
Currently Selected:
Eze 46: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979