YouVersion Logo
Search Icon

Eze 48

48
Rarraba Ƙasar
1“Ga sunayen kabilan da rabon gādonsu. Yankin Dan, shi ne daga iyakar arewa daga tekun. Ya bi ta Hetlon zuwa ƙofar Hamat, har zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu daga arewa, daura da Hamat. Ya zarce daga gabas zuwa yamma. 2Yankin Ashiru yana kusa da yankin Dan, daga gabas zuwa yamma. 3Yankin Naftali yana kusa da yankin Ashiru daga gabas zuwa yamma. 4Yankin Manassa yana kusa da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma. 5Yankin Ifraimu yana kusa da yankin Manassa daga gabas zuwa yamma. 6Yankin Ra'ubainu yana kusa da yankin Ifraimu daga gabas zuwa yamma. 7Yankin Yahuza yana kusa da yankin Ra'ubainu daga gabas zuwa yamma.
8“Kusa da yankin Yahuza daga gabas zuwa yamma, sai yankin da za ku keɓe. Faɗinsa kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), tsawonsa kuma daidai da tsawon yankunan kabilai daga gabas zuwa yamma. Haikali zai kasance a tsakiyar yankin.
9“Yankin da za ku keɓe wa Ubangiji, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗinsa kuwa kamu dubu goma (10,000). 10Wannan tsattsarkan yanki shi ne rabon firistoci. Tsawonsa wajen arewa, kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000) ne, faɗinsa a wajen yamma kuwa, kamu dubu goma (10,000) ne, a wajen gabas faɗinsa kamu dubu goma (10,000), a wajen kudu tsawonsa kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000). Haikalin Ubangiji zai kasance a tsakiyarsa. 11Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci daga zuriyar Zadok waɗanda suka kiyaye umarnina, ba su karkace kamar yadda Lawiyawa suka yi lokacin da jama'ar Isra'ila suka karkace ba. 12Zai zama rabonsu daga tsattsarkan yankin ƙasar da take kusa da yankin Lawiyawa. 13Gab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗi kuma kamu dubu goma (10,000). Tsawonsa duka zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗi kuwa kamu dubu goma (10,000). 14Daga cikinsa ba za su sayar ba, ko su musayar, ba kuma za su jinginar da wannan keɓaɓɓen yankin ƙasa ba, gama tsattsarka ne na Ubangiji.
15“Ragowar yankin mai faɗin kamu dubu biyar (5,000), da tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), zai zama hurumin birnin, inda za a yi gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar yankin. 16Ga yadda girman birnin zai kasance, a wajen arewa kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500), a wajen kudu kuwa kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500), a wajen gabas kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500), a wajen yamma kuma kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500). 17Birnin zai kasance da hurumi a kewaye da shi. A wajen gabas kamu metan da hamsin, a wajen yamma kamu metan da hamsin, a wajen kudu kamu metan da hamsin, a wajen arewa kuma kamu metan da hamsin. 18Ragowar tsawon yankin da yake gab da tsattsarkan yankin, zai zama kamu dubu goma (10,000) a wajen gabas, a wajen yamma kamu dubu goma (10,000). Amfanin da yankin zai bayar, zai zama abincin ma'aikatan birnin. 19Ma'aikatan birnin za su samu daga dukan kabilan Isra'ila, za su noma yankin.
20“Dukan yankin da za ku keɓe zai zama murabba'i mai kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), wato tsattsarkan yankin tare da hurumin birnin.
21“Ragowar kowane gefe na tsattsarkan yankin da hurumin birnin, zai zama na sarki. Tun daga kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000) na tsattsarkan yankin, zuwa iyakar da take wajen gabas, daga kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000) kuma zuwa iyakar wajen yamma, hannun riga da yankunan kabilan zai zama na sarki. Tsattsarkan yankin da wuri mai tsarki na Haikali za su kasance a tsakiyarsa. 22Rabon Lawiyawa da hurumin birnin za su kasance a tsakiyar yankin da yake na ɗan sarki. Yankin ɗan sarki zai kasance a tsakanin yankin Yahuza da yankin Biliyaminu.
23“Sauran kabilan kuwa za su samu. Biliyaminu zai sami yankinsa daga gabas zuwa yamma. 24Yankin Saminu yana kusa da yankin Biliyaminu daga gabas zuwa yamma. 25Yankin Issaka yana kusa da yankin Saminu daga gabas zuwa yamma. 26Yankin Zabaluna yana kusa da yankin Issaka daga gabas zuwa yamma. 27Yankin Gad yana kusa da yankin Zabaluna daga gabas zuwa yamma.
28“Kusa da yankin Gad zuwa kudu, iyakar za ta bi ta Tamar zuwa ruwan Meriba-kadesh, sa'an nan ta bi rafin Masar zuwa Bahar Rum.”
29Ubangiji ya ce, “Wannan ita ce hanyar da za ku raba gādo tsakanin kabilan Isra'ila. Waɗannan kuwa su ne yankunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
Ƙofofin Birni
30 # W.Yah 21.12,13 “Ƙofofin birnin a gefen arewa, kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500] ne. 31Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Ra'ubainu, da Ƙofar Yahuza, da Ƙofar Lawi. Ana kiran sunayen ƙofofin birnin da sunayen kabilan Isra'ila. 32A gefen gabas, kamu dubu huɗu ne da ɗari biyar (4,500). Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Yusufu, da Ƙofar Biliyaminu, da Ƙofar Dan. 33A gefen kudu, kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500). Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Saminu, da Ƙofar Issaka, da Ƙofar Zabaluna. 34A gefen yamma, kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500) ne. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Gad, da Ƙofar Ashiru, da Ƙofar Naftali. 35Da'irar birnin kamu dubu goma sha takwas (18,000) ne. Daga wannan lokaci za a kira birnin, ‘Ubangiji Yana Nan!’ ”

Currently Selected:

Eze 48: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in