Eze 45
45
Yankin Ƙasar da Za a Keɓe wa Ubangiji
1“Sa'ad da kuka rarraba ƙasar gādo, sai ku keɓe wa Ubangiji wani wuri domin ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗinsa kuwa kamu dubu goma (10,000). Dukan yankin zai zama wuri mai tsarki. 2Daga cikin wannan, murabba'i mai tsawo kamu ɗari biyar, da faɗi ɗari biyar, zai zama wuri mai tsarki, fili kuma mai kamu hamsin zai kewaye wurin nan mai tsarki. 3A cikin yanki mai tsarki za ka auna tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), da faɗi kamu dubu goma (10,000), inda Wuri Mafi Tsarki zai kasance. 4Wannan yanki shi ne zai zama wuri mai tsarki na ƙasar. Zai zama na firistoci waɗanda suke hidima a cikin Haikali, waɗanda suke kusatar Ubangiji don su yi masa hidima. Wurin zai zama wurin gina gidajensu da kuma wuri mai tsarki domin Haikalin. 5Wani sashi kuma mai tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), da faɗi kamu dubu goma (10,000), zai zama na Lawiyawa masu hidima cikin Haikalin, zai zama wurin da za su mallaka, su zauna a ciki. 6Za ku tsaga wa birnin hurumi mai fāɗi kamu dubu biyar, da tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), rabe da yankin nan mai tsarki. Hurumin zai zama na mutanen Isra'ila duka.”
Ƙasar Sarki
7“Ƙasar da take a sashin yankin nan mai tsarki, da hurumin birnin, zai zama na sarki. Zai zama hannun riga da yanki mai tsarki da hurumin birnin a wajen yamma da gabas. Tsawonta zai zama daidai da yanki ɗaya na yankunan kabilan. Za ta miƙe daga yamma zuwa iyakar ƙasar daga gabas. 8Wannan zai zama yankin ƙasarsa a cikin Isra'ila. Sarakunana kuma ba za su ƙara zaluntar mutanena ba, amma za su ba mutanen Isra'ila ƙasar bisa ga kabilansu.”
Ma'aunai na Gaskiya
9“Ni Ubangiji Allah na ce ku sarakunan Isra'ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari'a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.
10 #
L.Fir 19.36
“Sai ku kasance da ma'aunai na gaskiya, kamar su mudu da garwa.
11“Kwanon awo na mudu da na garwa girmansu ɗaya ne. Garwa goma ganga guda ne. Ganga ita ce za ta zama fitaccen ma'auni.
12“Shekel zai zama gera ashirin. Mainanku ɗaya zai zama shekel sittin.”
Hadayu da Sadakoki
13“Wannan ita ce bayarwar da za ku yi. Za ku ba da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta alkama, da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta sha'ir. 14Za ku ba da ɗaya daga cikin goma ta garwa daga kowace ganga ta mai. Ganga tana cin garwa goma. 15Za ku ba da tunkiya ɗaya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu, a cikin Isra'ila.
“Waɗannan su ne hadayu na gari, da na ƙonawa, da na salama, domin a yi musu kafara, ni Ubangiji Allah na faɗa.
16“Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwar domin Sarkin Isra'ila. 17Sarki ne da nawayar ba da hadayun ƙonawa, da na gari, da na sha a lokacin idodi da na amaryar wata, da ranakun Asabar, da lokacin dukan ƙayyadaddun idodin mutanen Isra'ila. Zai kuma ba da hadayu don zunubi da na salama domin a yi wa mutanen Isra'ila kafara.”
Idin Ƙetarewa
18“Ni Ubangiji Allah na ce, rana ta fari ga watan fari, za ku ɗauki bijimi marar lahani don a tsarkake Haikalin. 19Firist zai ɗibi jinin hadaya domin zunubi ya shafa shi a madogaran ƙofar Haikalin, da kusurwa huɗu na dakalin bagaden, da ginshiƙan ƙofar fili na can ciki. 20Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan, saboda wanda ya yi laifi da kuskure, ko da rashin sani. Ta haka ne za ku yi wa Haikalin kafara.
21 #
Fit 12.1-20; L.Ƙid 28.16-25 “A kan rana ta goma sha huɗu ga watan fari kuma za ku kiyaye Idin Ƙetarewa. Za ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai. 22A ranar, sarki zai ba da bijimi domin kansa da jama'ar ƙasar, saboda yin hadaya don zunubi. 23A ranaku bakwai na Idin, zai ba da bijimi bakwai da raguna bakwai marasa lahani hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Kowace rana kuma zai ba da bunsuru hadaya don zunubi. 24Zai kuma ba da hadaya ta gari, mudu guda domin kowane bijimi, da mudu guda domin kowane rago, da wajen kwalaba shida na mai tare da kowane mudu.
25 #
L.Fir 23.33-36; L.Ƙid 29.12-38 “A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, zai kuma ba da abubuwan nan har kwana bakwai domin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari game da mai.”
Currently Selected:
Eze 45: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979