Eze 44
44
Hidimar Haikali
1Ya kuma komo da ni ƙofar waje ta Haikali wadda take wajen gabas. Ƙofar kuwa tana rufe. 2Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofa za ta kasance a rufe, ba za a buɗe ta ba, ba wanda kuma zai shiga ta cikinta, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya shiga ta cikinta, saboda haka za ta kasance a rufe. 3Sai dai ɗan sarki zai zauna a cikinta ya ci abinci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin ƙofar, ya kuma fita ta wannan shirayi.”
4Sa'an nan ya kawo ni a gaban haikalin ta hanyar ƙofar arewa. Da na duba, na ga zatin Ubangiji cike da Haikalin, sai na faɗi rubda ciki. 5Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka gani da idanunka, ka kuma ji da kunnuwanka dukan abin da zan faɗa maka a kan dukan ka'idodin Haikalin Ubangiji da dukan dokokinsa. Ka lura sosai da waɗanda aka yardar musu su shiga Haikalin, da waɗanda ba a yarda musu su shiga ba.
6“Ka ce wa 'yan tawaye, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Ku daina ayyukanku na banƙyama. 7Gama kuna ƙazantar da Haikalina ta wurin shigar da baƙi marasa imani da marasa kaciya, sa'ad da kuke miƙa mini hadayu na kitse da jini. Kun ta da alkawarina da ayyukanku na banƙyama. 8Ba ku lura da hidimomina masu tsarki ba, amma kuka sa baƙi su lura da wurina mai tsarki.’ ”
9Ubangiji Allah ya ce, “Ba wani baƙo marar imani da marar kaciya, daga cikin dukan baƙin da suke cikin jama'ata Isra'ila da zai shiga wurina mai tsarki.
10“Amma Lawiyawa waɗanda suka yi nisa da ni, suka rabu da ni, suna bin gumakansu, sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkata, za su ɗauki alhakin muguntarsu. 11Za su zama masu hidima a cikin wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin Haikali, suna hidima a cikin Haikalin. Za su yanka hadayar ƙonawa da ta sadaka domin mutane. Za su lura da mutanen, su yi musu hidima. 12Da yake sun hidimta wa mutane a gaban gumakansu, suka zama sanadin mugun tuntuɓe ga mutanen Isra'ila, don haka ni Ubangiji Allah, na yi rantsuwa cewa za su karɓi hakkin muguntarsu. 13Ba za su zo kusa da ni a matsayin firistoci don su yi mini hidima ba. Ba za su zo kusa da abubuwana masu tsarki ba, amma za su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama. 14Amma duk da haka zan sa su lura da Haikalin, su yi dukan hidimomin da za a yi a cikinsa.
15“Amma Lawiyawan da suke firistoci daga zuriyar Zadok, waɗanda suka lura da Wuri Mai Tsarki sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkace, suka bar bina, su ne za su zo kusa da ni, su yi mini hidima, za su kusace ni domin su miƙa hadaya ta kitse da jini, ni Ubangiji Allah na faɗa. 16Za su shiga Wuri Mai Tsarki, su kusaci teburina, su yi mini hidima, su kuma kiyaye umarnina. 17#Fit 28.39-43; L.Fir 16.4 Sa'ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, sai su sa rigunan lilin, kada su sa abin da aka yi shi da ulu, sa'ad da suke hidima a ƙofofin fili na can ciki, da cikin Haikalin. 18Za su naɗa rawunan lilin, su sa wandunan lilin. Kada su sa abin da zai sa su yi zuffa. 19#L.Fir 16.23 Sa'ad da suka fita zuwa filin da yake waje, wurin mutane, sai su tuɓe tufafin da suka yi hidima da su, su ajiye su a tsarkakakkun ɗakuna, sa'an nan su sa waɗansu tufafi domin kada su tsarkake mutane da tsarkakakkun tufafinsu.
20 #
L.Fir 21.5
“Ba za su aske kansu ba, ba kuma za su bar zankayensu su yi tsayi ba, sai su sausaye gashin kansu. 21#L.Fir 10.9 Kada firist ya sha ruwan inabi sa'ad da zai shiga fili na can ciki. 22#L.Fir 21.7,13,14 Ba za su auri gwauruwa ba, wato wadda mijinta ya rasu, ko sakakkiya, sai budurwa daga zuriyar Isra'ila, ko kuwa matar firist wanda ya rasu.
23 #
L.Fir 10.10
“Za su koya wa jama'ata bambancin halal da haram, su kuma nuna musu yadda za su rarrabe tsakanin tsattsarka da marar tsarki. 24Za su zama masu raba gardama, za su yanke magana bisa ga doka. Za su kiyaye idodina bisa ga tsarinsu. Za su kuma kiyaye ranakun Asabar masu tsarki.
25 #
L.Fir 21.1-4
“Ba za su kusaci gawa ba, don kada su ƙazantar da kansu, amma saboda mahaifi, ko mahaifiya, ko ɗa, ko 'ya, ko 'yar'uwar da ba ta kai ga yin aure ba, ko ɗan'uwa, sa iya ƙazantar da kansu. 26Bayan ya tsarkaka, sai ya dakata har kwana bakwai. 27A ranar da zai shiga Wuri Mai Tsarki, can fili na ciki, domin ya yi hidima a wurin, sai ya miƙa hadayarsa don zunubi, ni Ubangiji Allah na faɗa.
28 #
L.Ƙid 18.20
“Ba za su sami rabon gādo ba, gama ni ne rabon gādonsu. Ba za ku ba su abin mallaka a cikin Isra'ila ba, ni ne abin mallakarsu. 29#L.Ƙid 18.8-19 Za su ci hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya domin laifi, kowane keɓaɓɓen abu kuma cikin Isra'ila zai zama nasu. 30Dukan nunan fari, da kowace hadaya daga dukan hadayunku, za su zama na firistoci. Za ku ba firistoci tumun farinku don albarka ta kasance a gidajenku. 31#L.Fir 22.8 Firistoci ba za su ci mushen kowane irin tsuntsu ko dabba ba, ba kuma za su ci waɗanda wata dabba ta kashe ba.”
Currently Selected:
Eze 44: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979