YouVersion Logo
Search Icon

Eze 35

35
Annabci a kan Dutsen Seyir
1 # Ish 34.5-17; 63.1-6; Irm 49.7-22; Eze 25.12-14; Amos 1.11,12; Oba 1.1-14; Mal 1.2-5 Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir, ka yi annabci a kansa. 3Ka faɗa masa, ni Ubangiji Allah na ce,
“Ga shi, ina gāba da shi, wato Dutsen Seyir.
Zan miƙa hannuna gāba da shi,
Zan maishe shi kufai, in lalatar da shi.
4Zan lalatar da biranensa,
In maishe su kufai marar amfani,
Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.
5“Saboda ya riƙe ƙiyayya din din din, ya ba da mutanen Isra'ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, da lokacin da adadin horonsu ya cika, 6don haka, ni Ubangiji na ce, hakika zan sa a zub da jininsa. Mai zub da jini zai fafare shi, da yake shi ma ya zub da jini, domin haka mai zub da jini zai fafare shi. 7Zan mai da Dutsen Seyir kufai marar amfani. Zan kashe duk mai shiga ko mai fita a cikinsa. 8Zan cika duwatsunsa da gawawwaki. Waɗanda za a kashe da takobi za su faɗi a kan tuddansa, da cikin kwarurukansa, da cikin dukan kwazazzabansa. 9Zan maishe shi kufai marar amfani har abada. Ba wanda zai zauna a cikin biranensa. Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.
10“Da yake ya ce al'umman nan biyu, da ƙasashen nan biyu za su zama nasa, ya mallake su, ko da yake Ubangiji yana cikinsu, 11domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, hakika zan saka masa gwargwadon fushinsa, da kishinsa, da ƙiyayyar da ya nuna musu. Zan sanar da kaina a gare su sa'ad da na hukunta shi. 12Zai sani Ubangiji ne wanda ya ji dukan zarge zargen da ya yi wa duwatsun Isra'ila, da ya ce, ‘An maishe su kufai marar amfani, an ba mu su mu cinye!’ 13Na ji tsiwa da dukan surutan da ya yi mini.
14“Ni Ubangiji Allah zan maishe shi kufai marar amfani, domin dukan duniya ta yi farin ciki. 15Kamar yadda ya yi farin ciki saboda gādon jama'ar Isra'ila, da ya zama kufai marar amfani, haka nan zan yi da shi, wato Seyir. Zai zama kufai marar amfani, wato Dutsen Seyir da dukan Edom. Sa'an nan mutane za su sani ni ne Ubangiji!”

Currently Selected:

Eze 35: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in