Eze 34
34
Annabci a kan Makiyayan Isra'ila
1Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra'ila, ka ce musu, ‘Ku masu kiwon mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, kaito, kaito, ku masu kiwon mutanen Isra'ila, kuna kiwon kanku kawai! Ashe, ba makiyaya ne suke kiwon tumaki ba? 3Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba. 4Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji. 5#L.Ƙid 27.17; 1Sar 22.17; Mat 9.36; Mar 6.34 Sai suka warwatsu saboda rashin makiyayin kirki, suka zama abincin namomin jeji. 6Tumakina sun watse, suna yawo a kan dukan duwatsu da tuddai, sun warwatsu a duniya duka, ba wanda zai nemo su.’
7“Domin haka, ku ji maganata, ku makiyaya. 8Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Hakika da yake tumakina sun zama ganimar dukan namomin jeji, saboda rashin makiyayin kirki, makiyayana kuma ba su nemo su ba, amma suka yi kiwon kansu, ba su yi kiwon tumakin ba, 9to, ku makiyaya, sai ku saurara ga maganata. 10Ga shi, ina gāba da ku, zan nemi tumakina a hannunku. Zan hana ku yin kiwon tumakin, ku kuma ba za ku ƙara yin kiwon kanku ba. Zan ƙwace tumakina daga hannunku, domin kada su ƙara zama abincinku.’ ”
Makiyayi Mai Kyau
11“Ni Ubangiji Allah na ce, ni kaina zan nemi tumakina. 12Kamar yadda makiyayi yakan nemo tumakin da suka watse daga cikin garkensa, haka zan nemi tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu. 13Zan fito da su daga cikin sauran al'umma, in tattaro su daga ƙasashe dabam dabam, in kawo su ƙasarsu, in yi kiwonsu a kan tuddan Isra'ila, kusa da maɓuɓɓugai, da cikin dukan wuraren da mutane suke zaune a ƙasar. 14Zan yi kiwonsu a makiyaya mai kyau. Ƙwanƙolin tuddan Isra'ila zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a makiyaya mai kyau, za su yi kiwo a makiyaya mai dausayi a kan tuddan Isra'ila. 15Ni kaina zan yi kiwon tumakin, in ba su hutawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.
16“Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.
17“Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ku kuma garkena, zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin rago da bunsuru. 18A ganinku abu mai kyau ne, bayan da kun yi kiwo a makiyaya mai kyau, sa'an nan ku tattake sauran makiyayar da ƙafafunku? Sa'ad da kuka sha ruwa mai kyau, sai kuma ku gurɓata sauran da ƙafafunku? 19Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake da ƙafafunku, su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku!’
20“Saboda haka, ni, Ubangiji Allah, na ce, ‘Zan shara'anta tsakanin turkakkun tumaki da ramammu. 21Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku, har kun watsar da su. 22Zan ceci garken tumakina, ba za su ƙara zama ganima ba. Zan kuma shara'anta tsakanin tunkiya da tunkiya. 23#W.Yah 7.17 Zan sa musu makiyayi guda, wato bawana Dawuda. Zai yi kiwonsu, ya zama makiyayinsu. 24#Eze 37.24 Ni kuma, Ubangiji, zan zama Allahnsu. Bawana Dawuda kuwa zai zama sarkinsu.’ Ni Ubangiji na faɗa.
25“Zan yi alkawarin salama da su. Zan kuwa kori namomin jeji daga ƙasar, domin tumakin su zauna lafiya a jeji, su kwana cikin kurmi. 26Zan sa su, da wuraren da suke kewaye da tuduna dalilin samun albarka. Zan aiko da ruwan sama a lokacinsa, zai kuma zama ruwan albarka. 27Itatuwan saura za su yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani. Za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su. 28Ba za su ƙara zama ganimar al'ummai ba, namomin jejin ƙasar kuma ba za su cinye su ba. Za su yi zamansu lafiya, ba wanda zai tsorata su. 29Zan ba su gonaki masu dausayi don kada yunwa ta ƙara far musu a ƙasar, kada kuma su ƙara shan zargi wurin sauran al'umma. 30Za su sani ni Ubangiji Allahnsu, ina tare da su, mutanen Isra'ila kuwa su ne mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.
31“Ku tumakin makiyayata, ku mutane ne, ni kuwa Allahnku ne, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
Currently Selected:
Eze 34: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979