YouVersion Logo
Search Icon

Eze 36

36
Albarkar Ubangiji a kan Ƙasar Isra'ila a Gaba
1“Kai ɗan mutum, ka yi annabci a kan duwatsun Isra'ila, ka ce, ‘Ya duwatsun Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji.’ 2Ubangiji Allah ya ce, da yake maƙiya suna cewa, ‘Madalla, tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu,’ 3sai ka yi annabci ka ce, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Da yake sun maishe ku kufai marar amfani, sun kuma murƙushe ku ta kowace fuska, har kun zama abin mallakar sauran al'umma, kun zama abin magana da abin tsegumi ga mutane. 4Domin haka, ku duwatsun Isra'ila, sai ku ji maganar Ubangiji Allah. Ni Ubangiji Allah, na ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, da kufai, da yasaassun birane waɗanda suka zama ganima da abin ba'a ga al'umman da suke kewaye, 5ni, Ubangiji Allah, ina yin magana da zafin kishina gāba da sauran al'umma, da dukan Edom, gama da farin ciki da raini suka mallaki ƙasata, suka washe ta.’
6“Domin haka ka yi wa ƙasar Isra'ila annabci, ka ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al'ummai.’
7“Domin haka ni Ubangiji Allah na rantse, cewa al'umman da suke kewaye da ku su ma za su sha zargi. 8Amma ku, ya duwatsun Isra'ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanen Isra'ila, gama za su komo gida ba da jimawa ba. 9Ga shi, ni naku ne, zan juyo wurinku. Za a kafce ku, a yi shuka! 10Zan sa dukan mutanen Isra'ila su riɓaɓɓanya a cikinku. Za su zauna cikin biranen, su gina rusassun wurare. 11Zan sa mutum da dabba su yawaita a cikinku, su kuma ba da amfani. Zan sa a zauna a cikinku kamar dā, sa'an nan zan nuna muku alheri fiye da dā. Daga nan za ku sani, ni ne Ubangiji. 12Zan kuma sa mutanena, Isra'ila, su yi tafiya a kanku, za ku zama gādonsu, ba za ku ƙara kashe 'ya'yansu ba.
13“Ni Ubangiji Allah na ce, da yake mutane sukan ce muku, 'Kuna cinye mutane, kuna kuma kashe 'ya'yan al'ummarku, 14saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ba, ba kuwa za ku ƙara kashe 'ya'yan al'ummarku ba. Ni Ubangiji Allah na faɗa. 15Ba zan ƙara bari ku sha zargi wurin sauran al'umma ba, ba kuwa za ku ƙara shan kunya a gaban jama'a ba, ba kuma zan ƙara sa al'ummarku ta yi tuntuɓe ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
16Ubangiji Kuma ya yi magana da ni, ya ce, 17“Ɗan mutum, sa'ad da mutanen Isra'ila suka zauna a ƙasar kansu, sun ƙazantar da ita ta wurin hanyoyinsu da ayyukansu. Halinsu a gare ni ya zama kamar rashin tsarkin mace a lokacin hailarta. 18Sai na husata da su saboda jinin da suka zuba a cikin ƙasar, da kuma yadda suka ƙazantar da ƙasar da gumakansu. 19Na warwatsa su cikin al'ummai, suka kuwa warwatsu cikin ƙasashe. Na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu. 20Amma sa'ad da suka tafi cikin al'ummai, sai suka ɓata sunana mai tsarki a duk inda suka tafi. Sai mutane suka yi magana a kansu cewa, ‘Waɗannan jama'ar Ubangiji ne, amma dole ne su fita daga cikin ƙasarsa.’ 21Amma na damu saboda sunana mai tsarki wanda mutanen Isra'ila suka sa aka ɓata shi a wurin al'ummai inda suka tafi.
22“Domin haka sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ba saboda ku ba ne, ya mutanen Isra'ila, zan yi wani abu, amma saboda sunana mai tsarki wanda kuka ɓata a wurin al'ummai inda kuka tafi. 23Zan ɗauki fansa saboda sunana mai tsarki, mai girma, wanda aka ɓata a wurin al'ummai, ku kuma kuka ɓata shi a cikinsu. Al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na tabbatar da tsarkina a wurinku a kan idonsu. 24Zan kwaso ku daga cikin al'ummai, in tattaro ku daga dukan ƙasashe, in kawo ku cikin ƙasarku. 25Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku. 26#Eze 11.19,20 Zan ba ku sabuwar zuciya, in sa sabon ruhu a cikinku. Zan cire zuciya mai tauri daga gare ku, sa'an nan in sa muku zuciya mai taushi. 27Zan sa ruhuna a cikinku, in sa ku bi dokokina, ku kiyaye ka'idodina. 28Za ku zauna cikin ƙasar da na ba kakanninku. Za ku zama mutanena, ni kuma in zama Allahnku. 29Zan tsarkake ku daga dukan ƙazantarku. Zan kuma sa hatsi ya yi yalwa, ba zan bar yunwa ta same ku ba. 30Zan sa 'ya'yan itatuwa da amfanin gona su yalwata, don kada ku ƙara shan kunya saboda yunwa a wurin al'ummai. 31Sa'an nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau. Za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda muguntarku da ayyukanku na banƙyama. 32Ni Ubangiji Allah na ce, sai ku sani, ba saboda ku ba ne zan aikata wannan. Ku kunyata, ku gigita saboda hanyoyinku, ya mutanen Isra'ila!’ ”
33Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da zan tsarkake ku daga dukan muguntarku, zan sa ku zauna cikin biranenku, ku gina rusassun wurare. 34Ƙasar da take kufai a dā za ku kafce ta maimakon yadda take kufai a kan idon dukan masu wucewa. 35Za su ce, ‘Wannan ƙasa wadda take kufai a dā ta zama kamar gonar Aidan, ga kuma rusassun wuraren da suka zama kufai, da rusassun birane, yanzu ana zaune a cikinsu, an kuma gina musu garu.’ 36Sa'an nan al'umman da suka ragu kewaye da ku za su sani, ni Ubangiji na sāke gina rusassun wuraren da suka zama kufai. Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”
37Ubangiji Allah ya ce, “Ga abin da zan sa mutanen Isra'ila su roƙe ni, in yi musu. Za su roƙe ni in yawaita su kamar garken tumaki. 38Kamar garken tumaki na hadaya, kamar garken tumaki a Urushalima a lokacin ƙayyadaddun idodi, haka rusassun birane za su cika da ɗumbun mutane. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

Currently Selected:

Eze 36: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in