YouVersion Logo
Search Icon

Eze 11

11
An Tsauta wa Mugayen Shugabanni
1Sai Ruhu ya ɗaga ni sama, ya kai ni ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji wadda dake fuskantar gabas. Sai ga mutum ashirin da biyar a bakin ƙofar. A cikinsu na ga Yazaniya ɗan Azzur, da Felatiya ɗan Benaiya, shugabannin jama'a.
2Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da suke ƙulla mugunta, waɗanda suke ba da muguwar shawara a cikin birnin. 3Waɗanda suke cewa, ‘Lokacin gina gidaje bai yi kusa ba. Wannan birni tukunya ce mai ɓararraka, mu ne kuwa naman.’ 4Saboda haka ka yi musu annabci marar kyau, ka yi annabci, ya ɗan mutum!”
5Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya ce mini, “Ka ce, ‘In ji Ubangiji, haka kuke tunani, ku mutanen Isra'ila, gama na san abin da yake cikin zuciyarku. 6Kun kashe mutane da yawa a wannan birni, har kun cika titunansa da gawawwaki.’
7“Domin haka Ubangiji Allah ya ce, ‘Gawawwakin da kuka shimfiɗa a cikin birnin su ne naman, birnin kuwa shi ne tukunya mai ɓararraka, amma za a fitar da ku daga cikinsa. 8Kun tsorata saboda takobi, ni kuwa zan kawo muku takobi,’ in ji Ubangiji Allah. 9‘Zan fitar da ku daga cikin birnin, in bashe ku a hannun baƙi, zan hukunta ku. 10Za a kashe ku da takobi. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji. 11Birnin ba zai zama muku tukunya mai ɓararraka ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinsa ba. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila. 12Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, gama ba ku kiyaye dokokina da ka'idodina ba, amma kuka kiyaye ka'idodin sauran al'umma waɗanda suke kewaye da ku.’ ”
13Sa'ad da nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benaiya, ya rasu. Sai na faɗi rubda ciki na fashe da kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah, za ka ƙare sauran mutanen Isra'ila ƙaƙaf ne?”
Allah Ya Yi wa Waɗanda aka Kai Bautar Talala Alkawari
14Ubangiji kuwa ya yi magana da ni, ya ce, 15“Ɗan mutum, 'yan'uwanka, da danginka, da mutanenka da suke cikin bautar talala tare da kai, da dukan mutanen Isra'ila, su ne waɗanda mazaunan Urushalima suke ce musu, ‘Ku yi nisa da Ubangiji, mu aka mallakar wa wannan ƙasa.’
16“Domin haka, ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah na ce, ko da yake na kai su nesa tsakanin al'ummai, na warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama Haikali a gare su a ɗan lokaci, a ƙasashen da suka tafi.’
17“Saboda haka ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, zan tattaro ku daga cikin al'ummai, da ƙasashen da aka warwatsa ku, ni kuwa zan ba ku ƙasar Isra'ila.’ 18Sa'ad da suka koma a ƙasar za su kawar da dukan abin da ya ƙazantar da ita, da dukan irin abar ƙyama da take cikinta. 19#Eze 36.26-28 Zan ba su zuciya ɗaya, in kuma sa sabon ruhu a cikinsu. Zan kawar musu da zuciya ta dutse, in ba su zuciya mai taushi, 20domin su kiyaye dokokina, da ka'idodina, su aikata su. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu. 21Amma waɗanda zuciyarsu ta karkata zuwa ga bin ƙazantattun abubuwa masu banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, ni Ubangiji na faɗa.”
Ɗaukakar Ubangiji ta Rabu da Urushalima
22 # Eze 43.2-5 Sa'an nan kerubobin suka ɗaga fikafikansu tare da ƙafafunsu. Ɗaukakar Ubangiji kuwa tana bisa kansu. 23Sai ɗaukakar Ubangiji ta bar tsakiyar birni, ta tsaya a bisa kan dutse wanda yake wajen gabas da birnin. 24Ruhu kuwa ya ɗauke ni a cikin wahayi, ya kai ni Kaldiya wurin 'yan zaman talala. Sa'an nan wahayin da na gani ya rabu da ni. 25Sai na faɗa wa 'yan zaman talala dukan abin da Ubangiji ya nuna mini.

Currently Selected:

Eze 11: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in