YouVersion Logo
Search Icon

Eze 12

12
Kwatancin Kwashewarsu zuwa Bautar Talala
1Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2#Ish 6.9,10; Irm 5.21; Mar 8.18 “Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan 'yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su 'yan tawaye ne. 3Domin haka, ɗan mutum sai ka shirya kaya don zuwa zaman talala, sa'an nan ka tashi da rana a kan idonsu. Za ka ƙaura daga wurinka zuwa wani wuri a kan idonsu, watakila za su gane, cewa su 'yan tawaye ne. 4Za ka fitar da kayanka da rana a kan idonsu, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Kai kuma da kanka za ka tafi da maraice a kan idonsu, kamar yadda mutane masu tafiyar zaman talala sukan yi. 5Ka huda katanga a kan idonsu, sa'an nan ka fita daga ciki. 6A gabansu za ka ɗauki kayan, ka saɓa shi a kafaɗarka, ka tafi da shi da dare. Za ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na maishe ka alama ga jama'ar Isra'ila.”
7Na kuwa yi kamar yadda aka umarce ni. Na fitar da kayana da rana, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Da maraice na huda katanga da hannuwana, sa'an nan na fita da duhu, ina ɗauke da kayana a kafaɗa, a kan idonsu.
8Da safe kuwa Ubangiji ya yi mini magana, ya ce, 9“Ɗan mutum, ashe, mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan, ko suka ce maka, ‘Me kake yi?’ 10Ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Wannan jawabi ya shafi shugabannin Urushalima da dukan mutanen Isra'ila, waɗanda suke cikinta.’ 11Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku, kamar yadda na yi, haka za a yi da ku, za a kai ku bauta.’ 12Sarkin da yake cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa, ya fita da duhu. Zai huda katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada ya ga ƙasar da idanunsa. 13#2Sar 25.7; Irm 52.11 Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can. 14Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi, masu taimakonsa da sojojinsa ko'ina. Zan zare takobi in runtume su.
15“Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na watsa su cikin sauran al'umma da cikin ƙasashe. 16Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, da yunwa, da annoba, don su tuba, su hurta dukan ayyukansu na banƙyama a cikin al'ummai inda suka tafi. Za su sani ni ne Ubangiji.”
Kwatancin Annabin da Yake Rawar Jiki
17Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 18“Ɗan mutum, ka ci abincinka da rawar jiki, ka sha ruwanka da makyarkyata da damuwa. 19Ka faɗa wa mutanen ƙasar, cewa ni Ubangiji Allah na ce mutanen Urushalima da suke a ƙasar Isra'ila za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suke zaune cikinta. 20Biranen da ake zaune a cikinsu za su zama kufai, ƙasar kuma za ta zama kango, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”
Sanannen Karin Magana da Jawabi Marar Daɗi
21Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 22“Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da ake faɗa a ƙasar Isra'ila cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba’? 23Ka faɗa musu, ka ce ni Ubangiji Allah na ce zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba. Amma ka faɗa musu, cewa kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.
24“Wahayin ƙarya da dūbā na kiran kasuwa za su ƙare a Isra'ila. 25Gama ni Ubangiji zan yi magana, maganata kuwa za ta tabbata, ba za ta yi jinkiri ba, amma za ta tabbata a kwanakinku, ku 'yan tawaye. Zan yi magana, za ta kuwa tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”
26Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 27“Ɗan mutum, ga shi, mutanen Isra'ila suna cewa, ‘Wahayin da ya gani na wani lokaci ne can gaba, yana annabci a kan wani zamani ne na can.’ 28Domin haka ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji na ce maganata ba za ta yi jinkiri ba, amma maganar da na faɗa za ta tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”

Currently Selected:

Eze 12: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in