Eze 10
10
Ɗaukakar Ubangiji ta Rabu da Haikali
1 #
Eze 1.26; W.Yah 4.2 Da na duba sararin sama da yake bisa kawunan kerubobi, sai na ga wani abu ya bayyana kamar yakutu. Fasalinsa kamar na kursiyi. 2#W.Yah 8.5 Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da rigar lilin. “Ka shiga ƙarƙashin ƙafafun kerubobin, ka cika tafin hannunka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin, ka watsa bisa kan birnin.”
Na kuwa ga ya tafi. 3Kerubobin kuwa suna tsaye a gefen kudu na Haikalin a sa'ad da mutumin ya shiga, girgije kuma ya cika farfajiyar da take can ciki. 4Ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga kan kerubobin zuwa ƙofar Haikalin. Girgije kuwa ya cika Haikalin, hasken zatin Ubangiji ya cika farfajiyar. 5Sai aka ji amon fikafikan kerubobin a filin da yake can waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa'ad da yake magana.
6Ya kuwa umarci wanda yake saye da lilin ɗin, ya ce, “Ka ɗibi wuta daga ƙarƙashin ƙafafun da suke tsakanin kerubobin.” Sai ya tafi ya tsaya a gefen ƙafar. 7Kerub kuwa ya miƙa hannunsa daga tsakanin kerubobi zuwa wurin wutar da take tsakanin kerubobin, ya ɗebo wutar, ya zuba a ahannun mutumin da yake saye da rigar lilin. Shi kuwa ya karɓa, ya fita.
8Kerubobin suna da hannuwa kamar na 'yan adam a ƙarƙashin fikafikansu. 9#Eze 1.15-21 Da na duba, sai na ga ƙafa guda huɗu kusa da kerubobin. Kowane kerub yana da ƙafa ɗaya kusa da shi. Ƙafafun suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja. 10Dukansu kuwa kamanninsu ɗaya, kamar ƙafa a cikin ƙafa. 11Sa'ad da suke tafiya, sukan tafi kowane waje, ba sai sun juya ba. Duk wajen da ƙafar gaba ta nufa, nan sauran za su bi, ba sai sun juya ba. 12#W.Yah 4.8 Suna da idanu a jikunansu ko'ina, a bayansu, da hannuwansu, da fikafikansu da kuma ƙafafunsu. 13Na ji ana kiran ƙafafun, ƙafafun guguwa.
14 #
Eze 1.10; W.Yah 4.7 Kowane kerub yana da fuska huɗu. Fuska ta fari ta kerub ce, fuska ta biyu ta mutum ce, fuska ta uku ta zaki ce, fuska ta huɗu kuwa ta gaggafa ce. 15Kerubobin kuwa suka tashi sama. Waɗannan su ne talikai huɗu waɗanda na gani a bakin kogin Kebar. 16Sa'ad da kerubobin suka tafi, ƙafafun kuma sukan tafi tare da su. Sa'ad da suka ɗaga fikafikansu don su tashi daga ƙasa zuwa sama, ƙafafun kuma ba su barinsu. 17Sa'ad da suka tsaya cik, sai ƙafafun su ma su tsaya cik, sa'ad da suka tashi sama, sai su kuma su tashi tare da su, gama ruhun talikan yana cikinsu.
18Sai ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga bakin ƙofar Haikalin, ta tsaya bisa kerubobin. 19Kerubobin kuwa suka ɗaga fikafikansu, suka tashi daga ƙasa, suka yi sama a kan idona, suka tafi da ƙafafun gab da su. Suka tsaya a ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji. Ɗaukakar Allah na Isra'ila kuwa tana bisa kansu. 20Waɗannan su ne talikan da na gani a ƙarƙarshin kursiyin Allah na Isra'ila a bakin kogin Kebar, na kuwa sani su kerubobi ne.
21Kowannensu yana da fuska huɗu, da fiffike huɗu. A ƙarƙashin fikafikansu suna da hannuwa irin na 'yan adam. 22Kamannin fuskokinsu kuma daidai yake da kamannin fuskokin da na gani a bakin kogin Kebar. Sai suka tafi, kowa ya nufi gabansa sosai.
Currently Selected:
Eze 10: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979