1
M.Had 7:9
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ka kame fushinka, Gama wawa ne yake cike da fushi.
Compare
Explore M.Had 7:9
2
M.Had 7:14
In kana jin daɗi, ka yi murna, In kuma wahala kake sha, ka tuna, Allah ne ya yi duka biyunsa, Don kada mutum ya san abin da zai faru a nan gaba.
Explore M.Had 7:14
3
M.Had 7:8
Gara ƙarshen abu da farkonsa. Mai haƙuri kuma ya fi mai girmankai.
Explore M.Had 7:8
4
M.Had 7:20
Ba wani mutum a duniyan nan wanda yake aikata abin da yake daidai dukan lokaci, ba tare da yin kuskure ba.
Explore M.Had 7:20
5
M.Had 7:12
Hikima mafaka ce, takan kāre mutum kamar yadda kuɗi yake yi. Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita, ita ce amfanin ilimi.
Explore M.Had 7:12
6
M.Had 7:1
Kyakkyawan suna ya fi man ƙanshi tsada, ranar mutuwa kuma ta fi ranar haihuwa.
Explore M.Had 7:1
7
M.Had 7:5
Gara mutum ya ji tsautawar mai hikima, Da ya ji wawaye suna yabonsa.
Explore M.Had 7:5
8
M.Had 7:2
Gara a tafi gidan da ake makoki Da a tafi gidan da ake biki, Gama wannan shi ne ƙarshen dukan mutane. Ya kamata duk mai rai ya riƙe wannan a zuciyarsa, Mutuwa tana jiran kowa.
Explore M.Had 7:2
9
M.Had 7:4
Mai hikima yakan yi tunanin mutuwa, Amma wawa yakan yi tunanin shagalin duniya.
Explore M.Had 7:4
Home
Bible
Plans
Videos