1
M.Had 4:9-10
Littafi Mai Tsarki
HAU
Biyu sun fi ɗaya, gama za su fi samun amfanin wahalar aikinsu. Gama idan ɗaya daga cikinsu ya fāɗi, ɗayan zai taimake shi ya tashi, amma idan ya faɗi yana shi kaɗai, to, tir, domin ba wanda zai taimake shi.
Compare
Explore M.Had 4:9-10
2
M.Had 4:12
Mutum biyu za su iya kāre kansu su ci nasara, amma mutum ɗaya ba zai iya kāre kansa ya ci nasara a kan wanda ya kawo masa hari ba. Igiya riɓi uku tana da wuyar tsinkawa.
Explore M.Had 4:12
3
M.Had 4:11
Idan mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna, amma ƙaƙa mutum ɗaya zai ji ɗumi?
Explore M.Had 4:11
4
M.Had 4:6
Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai, da tafin hannu biyu cike da tashin hankali, harbin iska ne kawai.
Explore M.Had 4:6
5
M.Had 4:4
Na gane dalilin da ya sa mutane suke aiki ƙwarai don su ci nasara, so suke su fi kowa samu. Wannan ma aikin banza ne harbin iska kawai.
Explore M.Had 4:4
6
M.Had 4:13-14
Mutum yana iya tashi daga matsayin talauci ya zama sarki a ƙasarsa, ko ya fita daga kurkuku ya hau gadon sarauta. Amma lokacin da sarki ya tsufa, idan wautarsa ta hana shi karɓar shawara, bai fi saurayin ɗin da yake talaka mai basira ba.
Explore M.Had 4:13-14
Home
Bible
Plans
Videos