1
M.Had 11:9
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ya saurayi! Ka yi murna a lokacin ƙuruciyarka, ka bar zuciyarka ta yi farin ciki a kwanakin samartakarka. Ka bi nufin zuciyarka da sha'awar idanunka. Amma ka sani fa, a cikin al'amuran nan duka Allah zai shara'anta ka.
Compare
Explore M.Had 11:9
2
M.Had 11:10
Kada ka bar kome ya dame ka, ko ya yi maka zafi a rai, gama ƙuruciya da samartaka ba za su dawwama ba.
Explore M.Had 11:10
3
M.Had 11:4
Wanda yake la'akari da iska, ba zai yi shuka ba, wanda kuma yake la'akari da gizagizai, ba zai yi girbi ba.
Explore M.Had 11:4
4
M.Had 11:5
Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda ƙasusuwan jariri suke girma a mahaifar uwarsa, haka nan kuma ba ka san aikin Allah ba, wato wanda ya yi abu duka.
Explore M.Had 11:5
5
M.Had 11:6
Ka shuka iri da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.
Explore M.Had 11:6
6
M.Had 11:2
Ka raba abin da yake hannunka ga mutum bakwai ko takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auka wa duniya ba.
Explore M.Had 11:2
Home
Bible
Plans
Videos