YouVersion Logo
Search Icon

Dan 10

10
Wahayin da Daniyel Yisa Gani a bakin Kogin Taigiris
1A shekara ta uku ta sarautar Sairus Sarkin Farisa, sai aka aiko da saƙo wurin Daniyel, wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar. Saƙon kuwa gaskiya ne, ya shafi zancen yaƙi, Daniyel kuwa ya fahimci saƙon.
2A waɗannan kwanaki, ni Daniyel, ina fama da baƙin ciki har mako uku. 3A makon nan uku ban ci wani abincin kirki ba, balle nama ko shan ruwan inabi, ban kuma shafa mai ba.
4A rana ta ashirin da huɗu ga watan fari, ina tsaye a gāɓar babban kogin Taigiris. 5#W.Yah 1.13-15; 2.18; 19.12 Da na ɗaga kaina sai na ga wani sāye da rigar lilin, ya ɗaura ɗamara ta zinariya tsantsa. 6Jikinsa kamar lu'ulu'u yake, fuskarsa kamar walƙiya, idanunsa kuma kamar harshen wuta, hannunwansa da ƙafafunsa kuwa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kamar ta babban taron jama'a.
7Ni kaɗai na ga wahayin, gama mutanen da suke tare da ni ba su ga wahayin ba, sai dai babbar razana ta auko musu, har suka gudu, suka ɓuya. 8Aka bar ni, ni kaɗai, na ga wannan babban wahayi, ni kuwa ba ni da sauran ƙarfi. Fuskata ta sauya, ta turɓune, ba ni da sauran ƙarfi. 9Sa'an nan na ji muryarsa, da jin muryarsa, sai na faɗi rubda ciki, barci mai nauyi ya kwashe ni.
10Sai hannu ya taɓa ni, ya tashe ni, sa'an nan hannuwana da gwiwoyina suna ta kaɗuwa. 11Ya ce mini, “Ya Daniyel, mutumin da ake sonka ƙwarai, ka lura da maganar da zan faɗa maka. Ka miƙe tsaye, gama a wurinka aka aiko ni.” Sa'ad da ya faɗi wannan magana, sai na miƙe tsaye, ina rawar jiki.
12Sai ya ce mini, “Kada ka ji tsoro, Daniyel, gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu'arka, amsar addu'arka ce ta kawo ni. 13#W.Yah 12.7 Shugaban ƙasar Farisa ya tare ni har kwana ashirin da ɗaya, amma Mika'ilu, ɗaya daga cikin shugabanni, ya zo ya taimake ni, ya tsaya wurin sarakunan Farisa. 14Na zo ne don in ganar da kai a kan abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin yana a kan kwanaki na nan gaba ne.”
15Sa'ad da ya faɗa mini wannan magana, na sunkuyar da kaina ƙasa, na yi shiru, ba magana. 16Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda yake tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi. 17Ƙaƙa zan iya magana da kai, ya shugabana? Yanzu ba ni da sauran ƙarfi, ba ni kuma da sauran numfashi.”
18Mai kamannin mutum ɗin nan kuma ya sake taɓa ni, ya kuma ƙarfafa ni. 19Ya ce, “Ya kai, mutumin da ake sonka ƙwarai, kada ka ji tsoro, salama a gare ka, ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali!”
Sa'ad da ya yi magana da ni, na sami ƙarfi na ce, “Yanzu sai shugabana ya yi magana, ka sa na sami ƙarfi.”
20Shi kuwa ya ce, “Ka san dalilin zuwana wurinka? Yanzu zan koma in yi yaƙi da shugaban Farisa, sa'ad da na murƙushe shi, shugaban Hellas zai taso. 21Zan faɗa maka abin da yake rubuce a littafin gaskiya. Ba wanda zai taimake ni yaƙi da waɗannan, sai dai Mika'ilu shugabanka.

Currently Selected:

Dan 10: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in