Dan 9
9
Daniyel Ya Yi Addu'a domin Mutanensa
1A shekara ta fari ta sarautar Dariyus ɗan Ahazurus Bamediye wanda ya ci sarautar Kaldiyawa, 2#Irm 25.11; 29.10 a wannan shekara ta sarautarsa ni Daniyel, ina nazarin littattafai, sai na ga labarin shekara saba'in ɗin nan da Ubangiji ya faɗa wa annabi Irmiya. Su ne yawan shekarun da Urushalima za ta yi tana zaman kango.
3Sai na mai da hankalina wajen Ubangiji Allah, ina nemansa ta wurin addu'a, da roƙe-roƙe tare da azumi, ina saye da tufafin makoki, na zauna cikin toka. 4Na yi addu'a ga Ubangiji Allahna, na tuba.
Na ce, “Ya Ubangiji, Allah maigirma, mai banrazana, kai mai cika alkawari ne, kana ƙaunar masu ƙaunarka waɗanda suke kiyaye dokokinka.
5“Mun yi zunubi, mun yi laifi, mun aikata mugunta, mun yi tawaye. Mun kauce daga bin umarnanka da ka'idodinka. 6Ba mu kasa kunne ga bayinka annabawa ba, waɗanda kuwa suka yi magana da sunanka ga sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, da dukan jama'ar ƙasa. 7Ya Ubangiji, kai mai adalci ne, amma mu sai kunya, kamar yadda yake a yau ga mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima da dukan Isra'ilawa, waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa a dukan ƙasashen da ka kora su saboda rashin amincin da suka yi maka. 8Ya Ubangiji kunya ta rufe mu, mu da sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, saboda mun yi maka zunubi. 9Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne mai gafara, amma mu, mun tayar masa. 10Ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ta wurin kiyaye dokokinsa ba, waɗanda ya ba mu ta hannun bayinsa annabawa. 11Dukan Isra'ilawa sun karya dokokinka, sun kauce, sun ƙi bin maganarka. La'ana da rantsuwa waɗanda suke a rubuce cikin dokokin Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi. 12Ya tabbatar da maganarsa wadda ya yi a kanmu da shugabanninmu waɗanda suka yi mulkinmu. Ya aukar mana da babban bala'i, gama a duniya duka ba a taɓa yin irin abin da aka yi wa Urushalima ba. 13Kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, haka wannan bala'i ya auko a kanmu, duk da haka ba mu nemi jinƙan Ubangiji Allahnmu ba, ba mu daina aikata muguntarmu ba, ba mu lizimci gaskiyarka ba. 14Domin haka Ubangiji ya shirya bala'i, ya kuma aukar mana da shi, gama Ubangiji Allahnmu mai adalci ne cikin dukan abin da ya aikata, amma mu ba mu bi maganarsa ba.
15“Ya Ubangiji Allahnmu, kai ne ka fito da jama'arka daga ƙasar Masar da iko mai girma, da haka ka bayyana ikonka kamar yadda yake a yau, amma mun yi zunubi, mun aikata mugunta. 16Ya Ubangiji, saboda dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hasalarka da ka yi da birninka Urushalima, tsattsarkan tudunka. Gama saboda zunubanmu da muguntar kakanninmu, Urushalima da jama'arka sun zama abin ba'a ga waɗanda suke kewaye da mu. 17Yanzu ya Allahnmu, ka ji addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Sabili da sunanka da idon rahama ka dubi tsattsarkan wurinka wanda ya zama kango. 18Ya Allahna, ka karkato kunnenka ka ji, ka buɗe idanunka ka ga yadda mu da birnin da ake kira da sunanka muka lalace. Ba cewa muna da wani adalci na kanmu shi ya sa muka kawo roƙe-roƙenmu ba, amma saboda yawan jinƙanka. 19Ya Ubangiji, ka ji mu. Ya Ubangiji, ka garfarce mu. Ya Ubangiji, ka saurare mu, ka yi wani abu saboda sunanka. Ya Allahna, kada ka yi jinkiri domin da sunanka ake kiran birninka da jama'arka.”
Annabci a kan Mako Saba'in
20Sa'ad da nake ta addu'a, ina faɗar zunubina, da na jama'ata Isra'ila, ina kawo roƙe-roƙena wurin Ubangiji Allahna saboda tsattsarkan tudun Allahna. 21#Luk 1.19,26 Sa'ad da nake yin addu'a, sai mutumin nan Jibra'ilu, wanda na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina a gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta maraice. 22Ya zo, ya ce mini, “Ya Daniyel, na zo ne don in ba ka hikima da ganewa. 23A lokacin da ka fara roƙe-roƙenka sai aka ba da umarni, na kuwa zo domin in faɗa maka, gama ana sonka ƙwarai. Sai ka fahimci maganar da wahayin.
24“An ƙayyade wa jama'arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa'in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa'an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake Haikali. 25Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara. 26Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Masihan, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara. 27#Dan 11.31; 12.11; Mat 24.15; Mar 13.14 Wannan shugaba zai yi alkawari mai ƙarfi na shekara bakwai da mutane da yawa. Amma bayan shekara uku da rabi za a hana a yi sadaka da hadaya. Abin ƙyama zai kasance a ƙwanƙolin Haikali, har lokacin da ƙaddara za ta auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”
Currently Selected:
Dan 9: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979