1Tim 3
3
Sharuɗan Zama Shugabannin Ikkilisiya
1Maganar nan tabbatacciya ce, cewa duk mai burin aikin kula da ikkilisiya, yana burin yin aiki mai kyau ke nan. 2#Tit 1.6-9 To, lalle ne mai kula da ikkilisiya yă zama marar abin zargi, yă zama mai mace ɗaya, mai kamunkai, natsattse, kintsattse, mai yi wa baƙi alheri, gwanin koyarwa kuma. 3Ba mashayi ba, ba mai saurin dūka ba, amma salihi, ba kuma mai husuma ba, ba kuwa mai son kuɗi ba. 4Lalle ne yă iya sarrafa iyalinsa da kyau, yana kuma kula da 'ya'yansa, su yi biyayya da matuƙar ladabi. 5Don kuwa in mutum bai san yadda zai sarrafa iyalinsa ba, ta ƙaƙa zai iya kula da ikkilisiyar Allah? 6Lalle ne kuma, kada yă zama sabon tuba, don kada yă daga kai yă burmu a cikin hukuncin da aka yi wa Iblis. 7Banda haka kuma, lalle ne yă zama mai mutunci ga waɗanda ba su a cikinmu, don kada yă zama abin zargi, yă faɗa a cikin tarkon Iblis.
Sharuɗan Zama Mai Hidimar Ikkilisiya
8Haka kuma masu hidimar ikkilisiya, lalle ne su zama natsattsu, ba masu baki biyu ba, ko mashaya, ko masu kwaɗayin ƙazamar riba. 9Lalle ne su riƙi asirin bangaskiya da lamiri mai tsabta. 10Sai an gwada su tukuna, in kuma an tabbata ba su da wani abin zargi, to, sai su kama aikin hidimar. 11Haka kuma matan, lalle su zama natsattsu, ba masu yanke ba, amma masu kamunkai, masu aminci ta kowace hanya. 12Masu hidima kuma su zama masu mata ɗaya ɗaya, masu sarrafa 'ya'yansu da sauran iyalinsu da kyau. 13Masu hidimar da suke aikinsu sosai, suna samar wa kansu kyakkyawan suna, da kuma ƙaƙƙarfar amincewa ga bangaskiyarsu ga Almasihu Yesu.
Asirin Addininmu
14Ina sa zuciya in zo a wurinka ba da daɗewa ba, amma ina rubuto maka waɗannan abubuwa. 15don in ya zamana na yi jinkiri, za ka san irin zaman da ya kamata a yi a jama'ar Allah, wadda take ita ce Ikkilisiyar Allah Rayayye, jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta. 16Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai,
An bayyana shi da jiki,
Ruhu ya nuna shi adali ne,
Mala'iku sun gan shi,
An yi wa al'ummai wa'azinsa,
An gaskata da shi a duniya,
An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.
Currently Selected:
1Tim 3: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979