1Tim 4
4
Faɗi a kan Malaman Ƙarya
1To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu, 2ta wurin makircin waɗansu maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu lalas. 3Su ne masu hana aure da cin abinci iri iri, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka ba da gaskiya, suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya. 4Domin duk abin da Allah ya halitta kyakkyawa ne, kada kuma a ƙi kome muddin an karɓe shi da godiya, 5gama an tsarkake shi ta wurin Maganar Allah da addu'a
Amintaccen Bawan Almasihu
6In kana tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa, za ka zama amintaccen bawan Almasihu Yesu, wanda aka goya da maganar bangaskiya, da kuma sahihiyar koyarwar nan wadda ka bi har ya zuwa yau. 7Ka ƙi tatsuniyoyin saɓo da na banza da wofi. Ka hori kanka ga bin Allah. 8Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba. 9Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum. 10Saboda wannan maƙasudi muke wahala, muke ta fama, domin mun dogara ne ga Allah Rayayye, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman masu ba da gaskiya.
11Ka yi umarni da waɗannan abubuwa, ka kuma koyar da su. 12Kada ka yarda kowa yă raina ƙuruciyarka, sai dai ka zama gurbi ga masu ba da gaskiya ta wurin magana, da hali, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsarkaka. 13Kafin in zo, ka lazamci karanta wa mutane Littattafai, da yin gargaɗi, da kuma koyarwa. 14Kada ka shagala da baiwar da aka yi maka, wadda aka ba ka ta wurin annabci, sa'ad da dattawan ikkilisiya suka ɗora maka hannu. 15Ka himmantu ga waɗannan abubuwa, ka kuma lazamce su ƙwarai, don kowa yă ga ci gaban da kake yi. 16Ka kula da kanka da kuma koyarwarka. Ka nace da haka, domin ta yin haka za ka ceci kanka da masu sauraronka.
Currently Selected:
1Tim 4: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979