YouVersion Logo
Search Icon

1Tim 2

2
Gargaɗi a kan Addu'a
1Da farko dai ina gargaɗi, cewa a yi ta roƙon Allah, ana addu'a, ana godo, ana gode wa Allah saboda dukkan mutane, 2da sarakuna da kuma duk waɗanda suke a manyan maƙamai, don mu zauna lafiya, rai a kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓa ne a gun Allah Mai Cetonmu, 4wanda yake son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya. 5Domin Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu, mutum, 6wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa. 7#2Tim 1.11 Don haka ne aka sa ni mai wa'azi, da manzo kuma (gasikya nake faɗa, ba ƙarya ba), mai koya wa al'ummai al'amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.
8Saboda haka, a kowane wuri ina so maza su yi addu'a, suna ɗaga hannuwa tsarkakakku, ba tare da fushi ko jayayya ba. 9#1Bit 3.3 Mata kuma su riƙa sa tufafin da suka dace da su saboda kunya da kamunkai, ba adon kitso, ko kayan zinariya, ko lu'ulu'u, ko tufafi masu tsada ba, 10sai dai su yi aiki nagari, yadda ya dace da mata masu bayyana shaidar ibadarsu. 11Mace ta riƙa koyo da kawaici da matuƙar biyayya. 12Ban yarda mace ta koyar, ko kuma ta yi iko da maza ba, sai dai ta zama shiru. 13#Far 2.7; Far 2.21,22 Ai, Adamu aka fara halitta, sa'an nan Hawwa'u. 14#Far 3.1-6 Ba kuma Adamu aka yaudara ba, amma matar ce aka yaudara, har ta keta umarni. 15Duk da haka kuwa, ta wurin haifar 'ya'ya sai ta kai ga kammala, muddin ta nace wa bangaskiya, da ƙauna, da zama a tsarkake, da kuma kamunkai.

Currently Selected:

1Tim 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy