1Bit 5
5
Ku Yi Kiwon Garken Allah
1Don haka, ku dattawan ikkilisiya da suke cikinku, ni da nike dattijon ikkilisiya, ɗan'uwanku, mashaidin shan wuyar Almasihu, mai samun rabo kuma a cikin ɗaukakar da za a bayyana, ina yi muku gargaɗi, 2#Yah 21.15-17 ku yi kiwon garken Allah da yake tare da ku, ba a kan tilas ba, sai dai a kan yarda, ba ma don neman ribar banza ba, sai dai da himma. 3Kada ku nuna wa waɗanda suke hannunku iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken nan. 4Sa'ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa. 5#K.Mag 3.34 Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”
6 #
Mat 23.12; Luk 14.11; 18.14 Don haka, sai dai ku ƙasƙantar da kanku ga maɗaukakin ikon Allah, domin ya ɗaukakaku a kan kari. 7Ku jibga masa dukan taraddadinku, domin yana kula da ku. 8Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis yana zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame. 9Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa a kan bangaskiyarku, da yake kun san 'yan'uwanku a duniya duka an ɗora musu irin wannan shan wuya. 10Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku. 11Mulki yā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!
Gaisuwa
12 #
A.M 15.22,40 Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan'uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi. 13#A.M 12.12,25; 13.13; 15.37-39; Kol 4.10; Fil 1.24 Ita da take a Babila, wadda ita ma zaɓaɓɓiya ce, ta aiko muku da gaisuwa. Haka kuma, ɗana, Markus. 14Ku gai da juna da sumbar ƙauna.
Salama tă tabbata a gare ku duka, ku na Almasihu.
Currently Selected:
1Bit 5: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979