YouVersion Logo
Search Icon

2Bit 1

1
Gaisuwa
1Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu. 2Alheri da salama su yawaita a gare ku, a wajen sanin Allah da Yesu Ubangijinmu
Kiranku da Zaɓenku
3Allah da ikonsa yā yi mana baiwa da dukan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma binsa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun ɗaukakarsa da fifikonsa, 4waɗanda kuma ta wurinsu ya yi mana baiwa da manyan alkawaransa masu ɗaukaka ƙwarai, domin ta wurin waɗannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen ɗabi'arsa, da yake kun tsira daga ɓācin nan dake a duniya da muguwar sha'awa take haifa. 5Saboda wannan dalili musamman, sai ku yi matuƙar himma, ku ƙara bangaskiyarku da halin kirki, halin kirki da sanin ya kamata, 6sanin ya kamata da kamunkai, kamunkai da jimiri, jimiri da bin Allah, 7bin Allah da son 'yan'uwa, son 'yan'uwa kuma da ƙauna. 8In kuwa halayen nan sun zama naku ne, har suna yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani a wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu. 9Domin duk wanda ya rasa halayen nan, to, makaho ne ko kuwa ganinsa dishi-dishi ne, ya kuma mance an tsarkake shi daga zunubansa na dā. 10Saboda haka, ya ku 'yan'uwa, ku ƙara ba da himma ku tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Domin in kun bi waɗannan halaye, ba za ku fādi ba har abada. 11Ta haka kuma, za a ba ku cikakken 'yancin shiga madawwamin mulki na Ubangijinmu Mai Cetonmu Yesu Almasihu.
12Don haka, lalle kullum ba zan fasa yi muku tunin waɗannan abubuwa ba, ko da yake kun san su, kun kuma kahu a kan gaskiyar nan da kuke da ita. 13A ganina daidai ne, muddin ina raye a cikin jikin nan, in riƙa faɗakar da ku ta hanyar tuni, 14da yake na sani na yi kusan rabuwa da jikin nan nawa, kamar yadda Ubangijinmu Yesu Almasihu ya yi mini ishara. 15Aniyata ce, a kowane lokaci ku iya tunawa da waɗannan abubuwa bayan ƙauracewata.
Ganin Ɗaukakarsa Muraran
16Ai, ba tatsuniyoyi da aka ƙaga da wayo muka bi ba, sa'ad da muka sanar da ku ikon Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma bayyanarsa, ɗaukakarsa ce muka gani muraran. 17#Mat 17.1-5; Mar 9.2-7; Luk 9.28-35 Domin sa'ad da Allah Uba ya girmama shi, ya kuma ɗaukaka shi, sai murya ta zo masa daga mafificiyar ɗaukaka cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai,” 18mu ne muka ji muryar nan da aka saukar daga sama, don muna tare da shi a kan tsattsarkan Dutsen nan. 19Har wa yau kuma, aka ƙara tabbatar mana da maganar annabcin nan, ya kuwa kyautu a gare ku, ku mai da hankali a gare ta, kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu har ya zuwa asubahin ranar nan, gamzaki kuma yă bayyana a zukatanku. 20Da farko dai, lalle ne ku fahimci wannan cewa, ba wani annabci a Littattafai da za a iya fassarawa ta ra'ayin mutum. 21Domin ba wani annabcin da ya taɓa samuwa ta nufin mutum, sai dai mutane ne Ruhu Mai Tsarki yake izawa, Allah yana magana ta bakinsu.

Currently Selected:

2Bit 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in