1Bit 4
4
Amintaccen Mai Riƙon Amanar Alherin Allah
1Tun da yake Almasihu ya sha wuya a jiki dominmu, sai ku ma ku ɗauki irin wannan ra'ayi. Ai, duk wanda ya sha wuya a jiki, ya daina aikata zunubi ke nan, 2domin a nan gaba yă ƙarasa sauran zamansa na jiki ba tare da biye wa muguwar sha'awar zuciya ba, sai dai nufin Allah. 3Lalle zaman da kuka yi na dā, irin wanda al'ummai suke son yi, ya isa haka nan, wato zaman fajirci, da mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa, da shashanci, da shaye-shaye, da kuma bautar gumaka, abar ƙyama. 4Suna mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, kuna zarmewa, kuna aikata masha'a irin tasu, har suna zaginku. 5Amma lalle su ba da hujjojinsu ga wannan da yake a shirye ya yi wa rayayyu da matattu shari'a. 6Shi ya sa aka yi bishara har ga matattu ma, waɗanda ko da yake an yi musu hukunci a cikin jiki kamar mutane, su samu su rayu a ruhu kamar Allah.
7Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku, ku natsu, domin ku yi addu'a. 8#K.Mag 10.12 Fiye da kome kuma, ku himmantu ga ƙaunar juna, domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa. 9Ku riƙa yi wa juna baƙunta, ba tare da ƙunƙuni ba. 10Duk baiwar da mutum ya samu, yă yi amfani da ita ga kyautata wa ɗan'uwansa, a kan amintaccen mai riƙon amanar alherin Allah iri iri ne. 11Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!
Shan Wuyar Kirista
12Ya ƙaunatattuna, kada ku yi mamakin matsananciyar wahalar da ta same ku a kan gwaji, kamar wani baƙon abu ne yake faruwa a gare ku. 13Amma, muddin kuna tarayya da Almasihu a wajen shan wuyarsa, sai ku yi farin ciki, domin sa'ad da aka bayyana ɗaukakarsa, ku yi farin ciki da murna matuƙa. 14Albarka ta tabbata a gare ku in ana zaginku saboda sunan Almasihu, don Ruhun ɗaukaka, wato Ruhun Allah yā tabbata a gare ku. 15Sai dai kada shan wuyar ko ɗaya daga cikinku ya zama na horon laifin kisankai ne, ko na sata, ko na mugun aiki, ko kuma na shisshigi. 16Amma in wani ya sha wuya a kan shi Kirista ne, to, kada ya ji kunya, sai dai ya ɗaukaka Allah saboda wannan suna. 17Don lokaci ya yi da za a fara shari'a ta kan jama'ar Allah. In kuwa ta kanmu za a fara, to, me zai zama ƙarshen waɗanda ba su bi bisharar Allah ba?
18 #
K.Mag 11.31
“In adali da ƙyar ya kuɓuta,
Me zai auku ga marar bin Allah da mai zunubi?”
19Saboda haka, sai duk masu shan wuya bisa ga nufin Allah su danƙa ransu ga Mahalicci mai aminci suna aikata abin da yake daidai.
Currently Selected:
1Bit 4: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979