1Sar 12
12
Mulki ya Rabu Biyu
(2Tar 10.1—11.4)
1Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan mutanen Isra'ila sun tafi Shekem don su naɗa shi sarki. 2Sa'ad da Yerobowam, ɗan Nebat, ya ji labari, gama a lokacin yana Masar inda ya gudu saboda sarki Sulemanu, sai ya komo daga Masar. 3Suka aika a kirawo shi, sai Yerobowam da dukan taron jama'ar Isra'ila suka zo suka ce wa Rehobowam, 4“Tsohonka ya nawaita mana, yanzu sai ka rage mana wahalar aikin tsohonka da nawayarsa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
5Sai ya ce musu, “Ku tafi, ku sāke zuwa bayan kwana uku.” Sai suka tafi.
6Sarki Rehobowam kuwa ya nemi shawara daga wurin dattawa, waɗanda suka bauta wa tsohonsa, Sulemanu, lokacin da yake da rai. Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan?”
7Suka ce masa, “Idan za ka zama mai lura da jama'an nan yau, ka bauta musu, sai ka yi musu magana da kyau, su kuwa za su zama talakawanka har abada.” 8Amma ya yi watsi da shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawara daga wurin matasa, tsararsa. 9Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan da suka roƙe ni wai in rage musu nawayar da tsohona ya aza musu?”
10Matasa da suke tsara ɗaya da shi kuwa suka ce masa, “Haka za ka faɗa wa mutanen nan da suka yi magana da kai, cewa tsohonka ya nawaita musu, amma sai ka sawwaƙa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri. 11Zan ƙara a kan nawayar da tsohona ya aza muku. Shi ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.’ ”
12Yerobowam da dukan mutane suka zo wurin Rehobowam a rana ta uku kamar yadda ya faɗa musu su zo wurinsa bayan kwana uku. 13Da suka zo, sai sarki ya yi musu magana da zafi, ya kuma yi watsi da shawarar da dattawa suka ba shi. 14Ya yi musu magana bisa ga shawarar matasa ya ce, “Tsohona ya nawaita muku, ni kuwa zan ƙara nawaita muku. Tsohona ya yi muku horo da bulala, amma ni zan yi muku da kunamai.” 15Haka kuwa sarki ya ƙi jin roƙon da jama'a suka yi masa, gama Ubangiji ne ya sa al'amarin ya zama haka domin ya cika maganarsa, wadda ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta bakin Ahija mutumin Shilo.
16 #
2Sam 20.1
Da mutanen Isra'ila suka ga sarki ya ƙi jin roƙonsu, sai suka yi ihu, suna cewa, “A yi ƙasa da Dawuda da iyalinsa. Me suka taɓa yi mana? Mazajen Isra'ila, bari duka mu tafi gida! Mu bar Rehobowam ya lura da kansa!”
Jama'ar Isra'ila fa suka tayar, 17suka bar Rehobowam ya sarauci jama'ar da take zaune a yankin ƙasar Yahuza.
18Sa'an nan sarki Rehobowam ya aiki Adoniram, shugaban aikin tilas, sai mutanen Isra'ila suka jajjefe shi da duwatsu har lahira. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta, ya hau karusarsa, ya tsere zuwa Urushalima. 19Da haka mutanen Isra'ila suka tayar wa gidan Dawuda har wa yau.
20Da dukan mutane suka ji, cewa Yerobowam ya komo, sai suka aika a kirawo shi ga taron jama'a. Suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka. Ba wanda ya bi gidan Dawuda, sai dai kabilar Yahuza.
21Da Rehobowam ya komo Urushalima, sai ya tara dukan jama'ar gidan Yahuza, da na kabilar Biliyaminu. Aka sami mayaƙa dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) waɗanda za su yi yaƙi da gidan Isra'ila, don su komar da su a ƙarƙashin mulkin Rehobowam, ɗan Sulemanu. 22Amma Ubangiji Allah ya yi magana da annabi Shemaiya, 23ya faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen gidan Yahuza da na Biliyaminu, da sauran jama'a, 24Ubangiji ya ce, “Kada ku haura zuwa yaƙi da 'yan'uwanku, mutanen Isra'ila, sai kowa ya koma gidansa, gama wannan al'amari daga wurina ne.” Su kuwa suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka koma gida.
Yerobowam Ya bar Bin Tafarkin Allah
25Sa'an nan sarki Yerobowam ya gina Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu, ya zauna can. Daga can kuma ya tafi ya gina Feniyel. 26Yerobowam kuwa ya ce a zuciyarsa, “Mulkin fa zai koma gidan Dawuda. 27Idan mutanen nan sun ci gaba da zuwa Urushalima don miƙa wa Ubangiji hadayu, zuciyarsu za ta koma kan sarki Rehobowam, na Yahuza, za su kashe ni, su koma wurinsa.”
28 #
Fit 32.4
Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.” 29Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan. 30Wannan abu ya zama zunubi, gama mutane sun tafi wurin siffofin maruƙan nan a Betel da Dan. 31Ya kuma gina masujadai a tuddai, sa'an nan ya sa waɗansu daga cikin mutane waɗanda ba Lawiyawa ba, su zama firistoci.
An Soki Sujada a Betel
32 #
L.Fir 23.33,34 Yerobowam kuma ya sa a yi idi ran goma sha biyar ga wata na takwas kamar yadda ake yi a Yahuza. Ya miƙa hadayu bisa bagade, haka ya yi a Betel. Ya yi ta miƙa hadayu ga siffofin maruƙan da ya yi. Ya kuma sa firistoci a masujadan da ya gina a Betel. 33Ya tafi gaban bagaden da ya gina a Betel a rana ta goma sha biyar ga wata na takwas, wato watan da ya zaɓa don kansa. Ya kafa wa jama'ar Isra'ila idi. Sai ya tafi don ya ƙona turare a kan bagaden.
Currently Selected:
1Sar 12: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979