1Sar 13
13
Annabi Ya Faɗakar da Yerobowam
1Bisa ga umarnin Ubangiji, sai ga annabi ya fito daga Yahuza zuwa Betel. Yerobowam kuwa yana tsaye kusa da bagaden don ya ƙona turare. 2#2Sar 23.15,16 Bisa ga umarnin Ubangiji, sai annabin ya ta da murya, ya ce, “Ya bagade, bagade, Ubangiji ya ce za a haifi ɗa a gidan Dawuda, sunansa Yosiya wanda zai miƙa firistoci na masujadan tuddai hadaya a kanka, wato firistoci waɗanda suke ƙona turare. Za a ƙone ƙasusuwan mutane a bisa kanka.” 3Ya kuma ba da alama a wannan rana cewa, “Wannan ita ce alamar da Ubangiji ya faɗa, za a rushe bagaden, a zubar da tokar da take bisansa.”
4Da sarki ya ji maganar annabin, wato wadda ya yi a kan bagaden da yake Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden, ya ce, “Ku kama shi.” Hannun da ya miƙa kuwa ya sage, bai iya komo da shi ba. 5Aka rushe bagaden, aka kuma zubar da tokar daga bagaden bisa ga alamar da annabin ya faɗa da sunan Ubangiji. 6Sarki Yerobowam ya ce wa annabin, “In ka yarda ka yi roƙo ga Ubangiji Allahnka domina, ka yi mini addu'a don ya warkar da hannuna.”
Annabi ya roƙi Ubangiji, sai hannun sarki ya komo daidai. 7Sa'an nan sarkin ya ce wa annabin, “Zo mu tafi gida don ka shaƙata, zan ba ka lada.”
8Annabin kuwa ya ce wa sarki, “Ko da za ka ba ni rabin gidanka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuma zan ci abinci ko in sha ruwa a wurin nan ba. 9Gama Ubangiji ya umarce ni da cewa kada in ci abinci, ko in sha ruwa, ko in koma ta hanyar da na zo.” 10Haka kuwa ya koma ta wata hanya dabam bai koma ta hanyar da ya bi zuwa Betel ba.
Tsohon Annabi na Betel
11Akwai wani tsohon annabi a Betel. 'Ya'yansa maza kuwa suka tafi suka faɗa masa dukan abin da annabin Allah ya yi a Betel a wannan rana. Suka faɗa wa mahaifinsu maganar da annabin Allah ya faɗa wa sarki. 12Tsohon annabin ya tambaye su, “Wace hanya ya bi?” Su kuwa suka nuna masa hanyar. 13Ya ce musu su ɗaura wa jakinsa shimfiɗa. Sai suka ɗaura wa jakin shimfiɗa, shi kuwa ya hau, 14ya bi bayan annabin nan da ya fito daga Yahuza, ya same shi yana zaune a gindin itace oak. Ya tambaye shi, “Ko kai ne annabin da ya zo daga Yahuza?”
Mutumin ya amsa, “I, ni ne,”
15Sa'an nan ya ce masa, “Zo mu tafi gida ka ci abinci.”
16Amma annabin ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba, ba kuwa zan shiga gida ba, ko in ci abinci, ko in sha ruwa tare da kai a wannan wuri, 17gama Ubangiji ya ce mini kada in ci abinci, ko in sha ruwa a can, ko in koma ta hanyar da na zo.”
18Sa, an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala'ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.
19Saboda haka sai annabin ya koma tare da shi, ya ci abinci, ya sha ruwa a gidan tsohon annabin. 20Sa'ad da suke zaune wurin ci, sai maganar Ubangiji ta zo ga tsohon annabin da ya komar da annabin Allah, 21sai ya kira annabin Allah, wanda ya zo daga Yahuza, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ba ka yi biyayya da maganar Ubangiji ba, ba ka kuma kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba, 22amma ka komo, ka ci abinci, ka sha ruwa a wurin da ya ce maka, kada ka ci abinci, ko kuwa ka sha ruwa, saboda haka ba za a binne gawarka a kabarin kakanninka ba.’ ”
23Bayan da ya ci abinci, ya sha sai tsohon annabin ya ɗaura wa jaki shimfiɗa don annabin da ya komo da shi. 24Sa'ad da annabin Allah ya tafi, sai zaki ya gamu da shi a hanya, ya kashe shi, ya jefar da gawarsa a kan hanya. Sai jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar. 25Mutane suka wuce, suka ga gawar a kan hanya, da zaki a tsaye kusa da gawar. Suka tafi suka faɗa a birni, inda tsohon annabin nan yake.
26Sa'ad da tsohon annabin nan ya ji, sai ya ce, “Wannan annabin Allah ne, wanda bai yi biyayya da maganar Ubangiji ba, saboda haka Ubangiji ya bashe shi ga zaki ya yayyage shi, ya kashe shi, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.” 27Sa'an nan ya ce wa 'ya'yansa maza, “Ku ɗaura mini shimfiɗa.” Su kuwa suka ɗaura, 28ya hau ya tafi, ya iske gawar a hanya. Jakin da zakin suna tsaye kusa da gawar. Zakin bai ci gawar ba, bai kuma fāɗa wa jakin ba. 29Tsohon annabin kuwa ya ɗauki gawar ya ɗora bisa jakin, ya kawo ta cikin birni, wato Betel, don yin makoki da binnewa. 30Ya binne gawar a kabarinsa, sa'an nan suka yi makoki suna cewa, “Kaito, dan'uwana!” 31Bayan da ya binne shi, sai ya ce wa 'ya'yansa, “Sa'ad da na rasu, sai ku binne ni a kabarin da aka binne annabin nan. Ku ajiye gawata kusa da tasa. 32Gama maganar Ubangiji da ya faɗa game da bagaden da yake cikin Betel, da masujadai na kan tuddai waɗanda suke a garuruwan Samariya, za ta cika.”
Zunubin Yerobowam zai Kai shi Hallaka
33Bayan wannan al'amari Yerobowam bai bar muguwar hanyarsa ba, amma ya naɗa firistoci daga cikin mutane don masujadai da suke kan tuddai. Duk mutumin da yake so, sai ya keɓe shi don ya zama firist na masujada da take kan tudu. 34Wannan zunubi ya zama sanadi ga gidan Yerobowam, har ya isa a shafe gidan, a hallaka shi ƙaƙaf.
Currently Selected:
1Sar 13: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979