1Sar 11
11
Sulemanu Ya Ridda
1 #
M.Sh 17.17
Sarki Sulemanu ya ƙaunaci baƙin mata. Banda 'yar Fir'auna, Sarkin Masar, ya auri matan Mowabawa, da na Ammonawa, da na Edomawa, da na Sidoniyawa, da na Hittiyawa. 2#Fit 34.16; M.Sh 7.3,4 Suna kuwa cikin al'umman da Ubangiji ya umarci jama'ar Isra'ila, ya ce, “Kada ku yi aurayya da su, gama hakika za su karkatar da zuciyarku zuwa gumakansu.” Sulemanu kuwa ya manne wa waɗannan mata da yake ƙauna. 3Ya auri mata ɗari bakwai, dukansu kuwa gimbiyoyi ne. Yana kuma da ƙwaraƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa kuwa suka janye zuciyarsa daga bin Ubangiji, 4sa'ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba. 5Gama Sulemanu ya bi Ashtoret ta Sidoniyawa, da Milkom, wato gunkin Ammonawa. 6Ya yi wa Ubangiji zunubi. Bai bi Ubangiji da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba. 7Sulemanu ya gina wa Kemosh, wato gunkin Mowab, da Molek, gunkin Ammonawa, masujadai a kan dutsen da yake gabas da Urushalima. 8Ya kuma gina masujadai inda dukan matansa baƙi za su riƙa miƙa turare da hadayu ga gumakansu.
9Ubangiji kuwa ya yi fushi da Sulemanu, domin zuciyar Sulemanu ta rabu da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya bayyana a gare shi sau biyu, 10ya kuma umarce shi kada ya bi gumaka. Amma bai kiyaye umarnin da Ubangiji ya yi masa ba. 11Saboda haka Ubangiji ya ce wa Sulemanu, “Tun da yake ka yi haka, ba ka kuwa kiyaye umarnina da dokokina waɗanda na umarce ka da su ba, to, hakika zan ƙwace mulki daga gare ka, in ba baranka. 12Amma saboda tsohonka, Dawuda, ba zan ƙwace a zamaninka ba, amma zan ƙwace daga hannun ɗanka. 13Duk da haka ba zan ƙwace mulkin duka ba, amma zan ba ɗanka kabila guda, saboda bawana Dawuda, saboda kuma Urushalima wadda na zaɓa.”
Abokan Gāban Sulemanu
14Ubangiji kuwa ya sa Hadad Ba'edome, ya tayar wa Sulemanu. Shi Hadad daga jinin sarautar Edom ne. 15Gama sa'ad da Dawuda ya ci Edom, Yowab, shugaban sojoji, ya tafi don ya binne kisassu, sun yi wata shida a can, shi da mutanensa, sai ya kashe kowane namijin da yake cikin Edom. 16Gama Yowab da dukan Isra'ilawa sun tsaya a Edom wata shida, sai da ya gama kashe mazajen Edom duka. 17Amma Hadad ya tsere zuwa Masar tare da waɗansu Edomawa, barorin tsohonsa. Hadad yana ɗan saurayi a lokacin. 18Suka kama hanya daga Madayana suka zo Faran. Daga Faran suka kwashi mutane tare da su, suka tafi Masar zuwa wurin Fir'auna, Sarkin Masar, wanda ya ba shi gida, ya kuma riƙa ba shi abinci, ya kuma ba shi ƙasa. 19Hadad kuwa ya sami farin jini ƙwarai a wurin Fir'auna, har ya aurar masa da ƙanwar matarsa, wato ƙanwar Tafenes, sarauniya. 20Ita kuwa ta haifa masa ɗa, Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a gidan Fir'auna. Genubat kuwa ya zauna tare da 'ya'yan Fir'auna, maza.
21Amma sa'ad da Hadad ya ji labari Dawuda ya rasu, Yowab shugaban sojoji shi ma ya rasu, sai Hadad ya ce wa Fir'auna, “Ka yardar mini, in tashi, in koma ƙasata.”
22Amma Fir'auna ya ce masa, “Me ka rasa a nan har da kake so ka koma ƙasarka?”
Hadad ya ce masa, “Ka dai yardar mini kawai in tafi.” Ya kuwa koma ƙasarsa.
23Allah kuma ya sa Rezon ɗan Eliyada, ya tayar wa Sulemanu, shi Rezon ya gudu daga wurin maigidansa, Hadadezer Sarkin Zoba. 24Ya tattara wa kansa mutane ya zama shugaban 'yan hari bayan kashe-kashen da Dawuda ya yi. Sai suka tafi Dimashƙu, suka zauna a can, suka naɗa shi Sarkin Dimashƙu. 25Ya zama abokin gāban Isra'ila a dukan zamanin Sulemanu. Ya yi ta ɓarna kamar yadda Hadad ya yi. Ya ƙi jinin mutane Isra'ila. Ya yi mulkin suriya.
Alkawarin Allah ga Yerobowam
26Sai Yerobowam ɗan Nebat, Ba'ifraime na Zaretan, baran Sulemanu, wanda sunan mahaifiyarsa Zeruya, wadda mijinta ya rasu, shi ma ya tayar wa sarki. 27Ga dalilin da ya sa ya tayar wa sarki.
Sulemanu ya gina Millo ya kuma faɗaɗa garun birnin Dawuda tsohonsa. 28Yerobowam mutum ne mai fasaha. Da Sulemanu ya ga shi saurayi ne mai himma, sai ya shugabantar da shi kan aikin tilas na gidan Yusufu. 29A sa'ad da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahija mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahija yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai, 30sai Ahija ya kama sabuwar rigar da ya sa, ya kyakketa ta ƙyalle goma sha biyu, 31ya ce wa Yerobowam, “Kwashi ƙyalle goma, gama haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, ina gab da in kece sarauta daga hannun Sulemanu, zan ba ka kabila goma. 32Amma Sulemanu, zai sami kabila ɗaya saboda bawana Dawuda, da kuma ɗaya saboda Urushalima, wato birnin da na zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka. 33Domin Sulemanu ya rabu da ni, ya bauta wa Ashtoret, gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh, gunkin Mowab, da Milkom, gunkin Ammonawa. Bai yi tafiya a cikin tafarkuna ba, bai yi abin da yake daidai a gare ni ba, bai kiyaye dokokina, da ka'idodina kamar yadda Dawuda, tsohonsa, ya yi ba. 34Duk da haka ba zan karɓe sarauta duka daga hannunsa ba, amma zan bar shi ya yi mulki muddin ransa saboda bawana Dawuda, wanda na zaɓa, wanda ya kiyaye umarnaina da dokokina. 35Amma zan karɓe mulki daga hannun ɗansa in ba ka, zan ba ka kabila goma. 36Duk da haka zan ba ɗansa kabila guda, domin bawana Dawuda ya kasance da fitila kullum a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa sunana. 37Zan sa ka yi mulki a kan duk abin da ranka yake bukata, za ka zama Sarkin Isra'ila. 38Idan za ka kasa kunne ga duk abin da na umarce ka, ka bi tafarkuna, ka aikata abin da yake daidai a gare ni, ka kiyaye dokokina da umarnaina kamar yadda bawana Dawuda ya yi, zan kasance tare da kai, zan sa gidanka ya kahu kamar yadda na sa gidan Dawuda ya kahu, zan ba ka Isra'ila. 39Zan wahalar da zuriyar Dawuda, amma ba har abada ba.’ ”
40Sulemanu kuwa ya nema ya kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tashi, ya tsere zuwa Masar, wurin Shishak Sarkin Masar, ya zauna a can har rasuwar Sulemanu.
Rasuwar Sulemanu
(2Tar 9.29-31)
41Sauran ayyukan Sulemanu, da dukan abin da ya yi, da hikimarsa an rubuta su a littafin tarihin Sulemanu. 42Sulemanu ya yi shekara arba'in yana sarauta a Urushalima a kan Isra'ila duka. 43Sulemanu ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda, wato Urushalima, ɗansa Rehobowam ya gaji sarautarsa.
Currently Selected:
1Sar 11: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979