YouVersion Logo
Search Icon

1Yah 5

5
Bangaskiya ta Yi Nasara da Duniya
1Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma. 2Ta haka muku sani muna ƙaunar 'ya'yan Allah, wato, in muna ƙaunar Allah, muna kuma bin umarninsa. 3#Yah 14.15 Domin ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne. 4Domin duk wanda yake haifaffen Allah yana nasara da duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta sa muka yi nasara da duniya. 5Wane ne yake nasara da duniya, in ba wanda ya gaskata Yesu Ɗan Allah ba ne?
Shaida a kan Ɗansa
6Shi ne wanda ya bayyana ta wurin ruwa da jini, Yesu Almasihu, ba fa ta wurin ruwa kaɗai ba, amma ta wurin ruwa da jini. 7Ruhu kuma shi ne mai ba da shaida, domin Ruhun shi ne gaskiya. 8Akwai shaidu uku, wato Ruhun, da ruwa, da kuma jini, waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce. 9Tun da yake muna yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. 10Kowa ya gaskata da Ɗan Allah, shaidar tana nan gare shi. Wanda bai gaskata Allah ba, ya ƙaryata shi ke nan, domin bai gaskata shaidar da Allah ya yi Ɗansa ba. 11#Yah 3.36 Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah yā ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. 12Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai. Wanda ba shi da Ɗan Allah kuwa, ba shi da rai.
Tabbatar Samun Rai Madawwami
13Na rubuto muku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan Ɗan Allah, domin ku tabbata kuna da rai madawwami. 14Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato, in mun roƙi kome bisa ga nufinsa, sai ya saurare mu. 15In kuwa muka san kome muka roƙa yana sauraronmu, mun tabbata mun sami abin da muka roƙa a gare shi ke nan. 16Kowa ya ga ɗan'uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai ya yi masa addu'a. Saboda mai addu'ar nan kuwa, Allah zai ba da rai ga waɗanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake na mutuwa. Ban ce a yi addu'a domin wannan ba. 17Duk rashin adalci zunubi ne. Akwai kuma zunubin da ba na mutuwa ba.
18Mun sani kowane haifaffen Allah ba ya yin zunubi, kasancewarsa haifaffen Allah ita takan kare shi. Mugun nan kuwa ba ta taɓa shi.
19Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.
20Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami. 21Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku yi nesa da gumaka.

Currently Selected:

1Yah 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy