YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 9

9
Waɗanda Suka Komo daga Babila
(Neh 11.1-24)
1Haka kuwa aka lasafta Isra'ilawa bisa ga asalinsu. An rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila.
Sai aka kai mutanen Yahuza zaman talala a Babila saboda rashin amincinsu ga Ubangiji. 2#Ezra 2.27; Neh 7.73 Waɗanda suka fara zama a biranen mallakarsu, su ne Isra'ilawa da firistoci, da Lawiyawa, da kuma ma'aikatan Haikali. 3Waɗansu mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na Ifraimu, da na Manassa suka zauna a Urushalima.
4-6Iyalin Yahuza guda ɗari shida da tasa'in suka zauna a Urushalima, shugabansu kuwa shi ne Utai ɗan Ammihud, jīkan Omri daga wajen Feresa. Waɗansu kakanninsu kuwa su ne Imri da Bani. Zuriyar Shela ɗan Yahuza suna da shugaba mai suna Asaya. Zuriyar Zera ɗan Yahuza kuwa, shugabansu Yuwel.
7Ga zuriyar Biliyaminu a Urushalima bi da bi, da Sallai ɗan Meshullam, da Hodawiya, da Hassenuwa, 8da kuma Ibneya ɗan Yeroham, da Ila ɗan Uzzi, wato jīkan Mikri, da Meshullam ɗan Shefatiya, da Reyuwel, da Ibnija.
9Tare da danginsu a zamaninsu, sun kai ɗari tara da hamsin da shida ne. Duk waɗannan shugabannin gidajen kakanninsu ne.
Firistocin da Suke a Urushalima
10Daga cikin firistoci masu zama a Urushalima su ne Yedaiya, da Yehoyarib, da Yakin, 11da Azariya ɗan Hilkiya, shi ne jami'in Haikalin Ubangiji, kakanninsa sun haɗu da Shallum ɗan Zadok, da Merayot, da Ahitub, 12da Adaya ɗan Yeroham, kakanninsa sun haɗu da Fashur, da Malkiya, da Ma'asai ɗan Adiyel, kakanninsa sun haɗu da Yazera, da Meshullam, da Meshillemot, da Immer.
13Firistacin da suke shugabannin gidajen kakanninsu, sun kai mutum dubu da ɗari bakwai da sittin (1,760). Ƙwararru ne cikin hidimar Haikalin Ubangiji.
14Lawiyawa masu zama a Urushalima kuma, su ne Shemaiya ɗan Hasshub, wanda kakanninsa suka haɗu da Azrikam da Hashabiya daga 'ya'yan Merari, maza, 15da kuma Bakbakkar, da Heresh, da Galal, da Mattaniya ɗan Mika wanda kakanninsa su ne Zikri da Asaf, 16da kuma Obadiya ɗan Shemaiya, kakanninsa su ne Galal da Yedutun, da Berikiya ɗan Asa, wato jīkan Elkana, wanda ya zauna a garin Netofa.
17Masu tsaron Haikalin, su ne Shallum, da Akkub, da Talmon, da Ahiman, da 'yan'uwansu. Shallum shi ne shugaba. 18Har zuwa yau, iyalinsu suke tsaron ƙofar sarki a wajen gabas. A dā su ne suke tsaron sauran ƙofofin zangon Lawiyawa.
19Shallum ɗan Kore, wato jīkan Ebiyasaf, tare da 'yan'uwansa na zuriyar Kora, suke lura da masu tsaron ƙofofin alfarwa kamar dai yadda kakanninsu suka lura da zangon Ubangiji. 20A dā Finehas ɗan Ele'azara shi ne shugabansu, Ubangiji kuwa yana tare da shi.
21Zakariya ɗan Shallum yake tsaron ƙofar alfarwa ta sujada.
22Dukan waɗanda aka zaɓa domin su zama masu tsaron ƙofofi, su ɗari biyu ne da goma sha biyu. An lasafta su bisa ga asalinsu da garuruwansu. Dawuda da Sama'ila annabi, su ne suka sa su a matsayinsu na riƙon amana. 23Saboda haka su da 'ya'yansu maza suke tsaron ƙofofin Ubangiji, wato alfarwa ta sujada. 24Matsaran ƙofofi suka tsaya a kusurwoyi huɗu, wato gabas da yamma, kudu da arewa. 25'Yan'uwansu waɗanda suke a ƙauyuka kuwa, ya zamar musu wajibi su zo wurinsu kowane kwana bakwai, domin su karɓe su tsaron. 26Su shugabanni huɗu na matsaran ƙofar Lawiyawa ne waɗanda suke da matsayi na riƙon amana, su ne masu lura da ɗakunan Haikalin Allah da dukiyarsa. 27Sukan kwana suna tsaro kewaye da Haikalin Allah, gama hakkin yana kansu. Su ne sukan buɗe shi kowace safiya.
28Waɗansunsu suna lura da kayayyakin aiki na cikin Haikali. Sukan ƙidaya su sa'ad da aka shigo da su, da sa'ad da aka fitar da su. 29Aka sa waɗansu su zama masu lura da kayayyakin Haikalin, da kayayyakin aiki na cikin Wuri Mai Tsarki, da lallausan gari, da ruwan inabi, da mai, da turare, da kayan yaji. 30Waɗansu 'ya'yan firistoci, maza, suke harhaɗa kayan yaji.
31Mattitiya, ɗaya daga cikin Lawiyawa, ɗan farin Shallum na iyalin Kora, shi ne mai lura da toya waina. 32Waɗansu 'yan'uwansu Kohatawa suke lura da gurasar ajiyewa. Sukan shirya ta kowace Asabar.
33Waɗannan su ne mawaƙa, da shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa, waɗanda suka zauna a ɗakunan Haikali, ba su yin wani aiki dabam, gama dare da rana suke yin aikinsu.
34Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa a zamaninsu, wato waɗanda suka zauna a Urushalima.
Kakannin Sarki Saul da Zuriyarsa
35Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a ciki, sunan matarsa Ma'aka, 36ɗan farinsa kuma shi ne Abdon. Sa'an nan ga Zur, da Kish, da Ba'al, da Ner, da Nadab, 37da Gedor, da Ahiyo, da Zakariya, da Miklot, 38mahaifin Shimeya. Zuriyarsu ne suka zauna a Urushalima daura da 'yan'uwansu.
39Ner ya haifi Kish, Kish kuma ya haifi Saul, Saul ya haifi Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet. 40Jonatan ya haifi Mefiboshet, Mefiboshet ya haifi Mika. 41'Ya'yan Mika, maza, su ne Fiton, da Melek, da Tareya, da Ahaz. 42Ahaz ya haifi Yehowadda, Yehowadda ya haifi Allemet, da Azmawet, da Zimri. Zimri ya haifi Moza, 43Moza ya haifi Bineya, da Refaya, da Eleyasa, da Azel.
44Azel yana da 'ya'ya maza guda shida, su ne Azrikam, da Bokeru, da Isma'ilu, da Sheyariya, da Obadiya, da Hanan.

Currently Selected:

1Tar 9: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in