YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 10

10
Mutuwar Sarki Saul da ta 'Ya'yansa
(1Sam 31.1-13)
1Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ilawa, Isra'ilawa suka gudu a gaban Filistiyawa, aka karkashe su a Dutsen Gilbowa. 2Filistiyawa suka kama Saul da 'ya'yansa maza, suka kashe Jonatan da Yishwi, da Malkishuwa. 3Yaƙin ya tsananta wa Saul, maharba suka rutsa Saul, suka yi masa rauni. 4Sai Saul ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Zare takobinka, ka kashe ni, don kada marasa kaciyan nan su zo su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar makamai nasa bai yarda ba, gama yana jin tsoro ƙwarai. Saboda haka sai Saul ya zare takobinsa ya fāɗi a kansa. 5Sa'ad da mai ɗaukar makamansa ya ga Saul ya mutu, sai shi ma ya faɗi a kan takobinsa ya mutu. 6Ta haka Saul ya mutu, shi da 'ya'yansa maza guda uku tare da dukan gidansa. 7Sa'ad da dukan Isra'ilawa waɗanda suke zaune a kwari suka ga sojojin sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa suka zo suka zauna a wurin.
8Kashegari, sa'ad da Filistiyawa suka tafi su kwashe waɗanda aka kashe, sai suka tarar da Saul da 'ya'yansa maza matattu a Dutsen Gilbowa. 9Suka kuwa tuɓe tufafinsa, suka datse kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka aiki manzanni ko'ina a ƙasar Filistiyawa don su ba gumakansu da jama'arsu wannan albishir. 10Sai suka ajiye kayan yaƙin Saul a gidan gumakansu, suka kuma rataye kansa a gidan gunkin nan, wato Dagon. 11Sa'ad da mutanen Yabesh-gileyad suka ji irin abin da Filistiyawa suka yi wa Saul, 12sai dukan ƙarfafan mutanensu suka tafi suka ɗauki gawar Saul, da gawawwakin 'ya'yansa, suka kawo a Yabesh suka binne ƙasusuwansu a ƙarƙashin itacen oak cikin Yabesh. Suka yi azumi har kwana bakwai.
13 # 1Sam 13.8-14; 15.1-24; L.Fir 19.31; 20.6; 1Sam 28.7,8 Haka nan Saul ya mutu saboda laifin da ya yi wa Ubangiji, gama bai kiyaye maganar Ubangiji ba, saboda kuma ya nemi shawara wurin masu mabiya. 14Amma bai nemi Ubangiji ba. Domin haka Ubangiji ya kashe shi, ya ɗauki sarautar, ya ba Dawuda ɗan Yesse.

Currently Selected:

1Tar 10: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in