1Tar 8
8
Zuriyar Biliyaminu
1Biliyaminu yana da 'ya'ya biyar, su ne Bela, da Ashbel, da Ahiram, 2da Noha, da Rafa.
3Bela kuma yana da 'ya'ya maza, su ne Adar, da Gera da Abihud, 4da Abishuwa, da Na'aman, da Ahowa, 5da Gera, da Shuffim, da Huram.
6Waɗannan kuma su ne 'ya'yan Ehud, maza. Su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu da suke zaune a Geba, waɗanda aka kai su bauta a Manahat. 7Ga sunayensu, Na'aman, da Ahaija, da Gera wanda yake shugabansu lokacin da aka kai su bauta. Shi ne kuma mahaifin Uzza da Ahihud.
8Shaharayim kuma yana da 'ya'ya maza a ƙasar Mowab bayan da ya saki matansa biyu, wato Hushim da Ba'ara. 9Matarsa Hodesh ta haifa masa 'ya'ya maza, su ne Yobab, da Zibiya, da Mesha, da Malkam, 10da Yuz, da Sakiya, da Mirma. Waɗannan su ne 'ya'yansa maza, shugabannin gidajen kakanninsu.
11Hushim kuma ta haifa masa waɗansu 'ya'ya maza, su ne Abitub da Elfayal.
12'Ya'yan Elfayal, su ne Eber, da Misham, da Shemed wanda ya gina Ono da Lod da ƙauyukansu, da 13Beriya, da Shimai, su ne shugabannin gidajen kakanninsu da suke zaune a Ayalon waɗanda suka kori mazaunan Gat, 14da Ahiyo, da Shashak, da Yeremot. 15Zabadiya, da Arad, da Eder, 16da Maikel, da Ishfa, da Yoha, su ne 'ya'yan Beriya, maza.
17Zabadiya, da Meshullam, da Hizki, da Eber, 18da Ishmerai, da Izliya, da Yobab, su ne zuriyar Elfayal.
19Zuriyar Shimai, su ne Yakim, da Zikri, da Zabdi, 20da Eliyenai, da Zilletai, da Eliyel, 21da Adaya, da Beraiya, da Shimrat.
22Zuriyar Shashak, su ne Isfan, da Eber, da Eliyel, 23da Abdon, da Zikri, da Hanan, 24da Hananiya, da Elam, da Antotiya, 25da Ifediya, da Feniyel.
26Zuriyar Yeroham, su ne Shemsherai, da Shehariya, da Ataliya, 27da Yawareshiya, da Eliya, da Zikri.
28Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakanninsu a zamaninsu, waɗanda suka zauna a Urushalima.
Zuriyar Saul
(1Tar 9.35-44)
29Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a can. Sunan matarsa Ma'aka. 30Abdon ne ɗansa na fari, sa'an nan Zur, da Kish, da Ba'al, da Nadab, 31da Gedor, da Ahiyo, da Zakariya, 32da Miklot, mahaifin Shimeya. Waɗannan su ne suka zauna daura da 'yan'uwansu a Urushalima.
33Ner shi ne mahaifin Kish, Kish kuma shi ne mahaifin Saul, Saul shi ne mahaifin Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet. 34Jonatan ya haifi Mefiboshet, Mefiboshet ya haifi Mika.
35'Ya'yan Mika, maza, su ne Fiton, da Melek, da Tareya, da Ahaz. 36Ahaz ya haifi Yehowadda, Yehowadda ya haifi Allemet, da Azmawet, da Zimri. Zimri ya haifi Moza. 37Moza ya haifi Bineya, da Refaya, da Eleyasa, da Azel.
38Azel ya haifi 'ya'ya maza su shida, su ne Azrikam, da Bokeru, da Ismayel, da Sheyariya, da Obadiya, da Hanan. 39'Ya'ya maza na Esheke ɗan'uwansa su ne, Ulam, da Yewush, da Elifelet.
40'Ya'yan Ulam, maza, jarumawa ne sosai, 'yan baka, suna da 'ya'ya maza, da jikoki maza da yawa. Su ɗari da hamsin ne. Waɗannan duka mutanen Biliyaminu ne.
Currently Selected:
1Tar 8: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979