YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 25

25
Ƙungiyoyin Mawaƙa
1Dawuda fa da shugabannin Lawiyawa suka zaɓi waɗansu daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, da na Heman, da na Yedutun domin su raira waƙa da garayu, da molaye, da kuge. Ga waɗanda suka yi wannan hidima.
2Daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, Zakkur, da Yusufu, da Netaniya, da Asharela, Asaf mahaifinsu ne yake bi da su, shi ne kuma mawaƙin sarki.
3Na wajen Yedutun, su ne 'ya'yan Yedutun, maza, wato Gedaliya, da Zeri, da Yeshaya, da Shimai, da Hashabiya, da Mattitiya, su shida ne. Mahaifinsu Yedutun shi ne yake bi da su, shi ne kuma mai raira waƙoƙi da garaya domin godiya da yabon Ubangiji.
4Na wajen Heman, su ne 'ya'yan Heman, maza, wato Bukkiya, da Mattaniya, da Uzziyel, da Shebuwel, da Yerimot, da Hananiya, da Hanani, da Eliyata, da Giddalti, da Romamti-yezer, da Yoshbekasha, da Malloti, da Hotir, da Mahaziyot. 5Allah ya ba Heman, wato annabin sarki, 'ya'ya maza su goma sha huɗu, da 'ya'ya mata su uku, kamar yadda ya yi alkawari, domin ya ba Heman iko. 6Dukansu tsohonsu ne yake bi da su da raira waƙoƙi, da kaɗa kuge, da molaye da garayu, cikin Haikalin Ubangiji, domin yin sujada. Asaf, da Yedutun, da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki. 7Jimillar horarrun mawaƙa don raira waƙa ga Ubangiji, su da 'yan'uwansu, duka waɗanda suke ƙwararru, su ɗari biyu da tamanin da takwas ne.
8Sai suka jefa kuri'a domin su ba kowa aikin da zai yi, yaro da babba, malami da almajiri.
9-31Waɗannan su ne shugabannin ƙungiyoyi ashirin da huɗu, na goma sha biyu biyu, bisa ga yadda aka tsara su ga aikin:
1. Yusufu daga iyalin Asaf
2. Gedaliya
3. Zakku
4. Zeri
5. Netaniya
6. Bukkiya
7. Asharela
8. Yeshaya
9. Mattaniya
10. Shimai
11. Uzziyel
12. Hashabiya
13. Shebuwel
14. Mattitiya
15. Yeremot
16. Hananiya
17. Yoshbekasha
18. Hanani
19. Malloti
20. Eliyata
21. Hotir
22. Giddalti
23. Mahaziyot
24. Romamtiyezer

Currently Selected:

1Tar 25: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in