YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 26

26
Masu Tsaron Haikali da Shugabanni
1Ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi ke nan. Na wajen Kora shi ne Shallum ɗan Kore, daga cikin iyalin Ebiyasaf. 2Shallum kuwa yana da 'ya'ya maza, su ne Zakariya, da Yediyayel, da Zabadiya, da Yatniyel, 3da Elam, da Yehohanan, da Eliyehoyenai, su bakwai ke nan.
4 # 2Sam 6.11; 1Tar 13.14 Obed-edom kuma Allah ya ba shi 'ya'ya maza, su ne Shemaiya, da Yehozabad, da Yowa, da Sakar, da Netanel, 5da Ammiyel, da Issaka, da Fauletai, da su Allah ya sa masa albarka.
6Ɗan farin Obed-edom, wato Shemaiya ya haifi 'ya'ya maza waɗanda suka yi shugabanci a gidan kakansu, gama su jarumawa ne. 7'Ya'yan Shemaiya, su ne Otni, da Refayel, da Obida, da Elzabad, waɗanda 'yan'uwansu, Elihu, da Semakiya jarumawa ne.
8Waɗannan duka iyalin Obed-edom ne. Su da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu suna da ƙarfi da gwaninta na yin aiki. Su sittin da biyu ne daga wajen Obed-edom.
9Shallum yana da 'ya'ya maza da 'yan'uwa, su goma sha takwas jarumawa.
10Hosa kuma na wajen 'ya'yan Merari, maza, yana da 'ya'ya maza, Shimri shi ne babba, ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, duk da haka mahaifinsa ya maishe shi babba. 11Hilkiya shi ne na biyu, da Tebaliya na uku, da Zakariya na huɗu. Dukan 'ya'yan Hosa, maza, da 'yan'uwansa, su goma sha uku ne.
12Aka rarraba masu tsaron Haikali ƙungiya ƙungiya, bisa ga iyali, aka raba musu ayyuka a Haikali kamar dai sauran Lawiyawa. 13Sai suka jefa kuri'a bisa ga gidajen kakanninsu, ba a damu da yawan jama'a a iyali ba, a kan kowace ƙofar. 14Kuri'a ta ƙofar gabas ta faɗo a kan Shallum. Sai aka jefa kuri'a don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma'ana, sai kuri'a ta ƙofar arewa ta faɗo a kansa. 15Kuri'a ta ƙofar kudu ta faɗo a kan Obed-edom. Aka sa 'ya'yansa maza su lura da ɗakunan ajiya. 16Kuri'a ta ƙofar yamma kusa da Ƙofar Shalleket, a kan hanyar da ta haura, ta faɗo a kan Shuffim da Hosa. Aka raba aikin tsaro bisa ga lokatan da aka tsara bi da bi. 17A kowace rana Lawiyawa shida suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu biyu suke tsaron ɗakunan ajiya. 18A ɗan ɗakin da take wajen yamma, akwai masu tsaro huɗu a hanyar, biyu kuma a ɗan ɗakin. 19Waɗannan su ne ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi daga zuriyar Kora da ta Merari.
Sauran Ayyukan Haikali
20Sauran Lawiyawa, 'yan'uwansu kuwa, suke lura da baitulmalin Haikalin Allah, da ɗakin ajiyar kayan da aka keɓe ga Allah. 21Libni daga cikin iyalin Gershon, shi ne kakan ƙungiyoyin iyali da dama, iyalin Yehiyel ne ɗaya daga cikinsu. 22Biyu daga cikin wannan iyali, wato Zetam da Yowel, suke lura da baitulmalin Haikali da ɗakin ajiyar kaya.
23Aka raba aiki kuma ga zuriyar Amram, da ta Izhara, da ta Hebron, da kuma ta Uzziyel.
24Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami'in baitulmalin. 25Ta wurin ɗan'uwan Gershom, wato Eliyezer ya sami dangantaka da Shelomit. Eliyezer shi ne mahaifin Rehabiya, wanda ya haifi Yeshaya, uban Yoram, da Zikri, da Shelomit. 26Shi wannan Shelomit da 'yan'uwansa suke lura da kyautai waɗanda sarki Dawuda, da shugabannin, gidajen kakanni, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da shugabannin sojoji suka keɓe ga Allah. 27Daga cikin ganimar yaƙi suka keɓe wani sashi domin gyaran Haikalin Ubangiji. 28Dukan kuma abin da Sama'ila annabi, da Saul ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruya, suka keɓe an sa su a hannun Shelomit da 'yan'uwansa.
Ayyukan Sauran Lawiyawa
29Kenaniya da 'ya'yansa maza na wajen Izhara su ne aka danƙa wa al'amuran sasantawa na Isra'ilawa, wato sun zama shugabanni da alƙalai.
30Hashabiya da 'yan'uwansu, su dubu da ɗari bakwai (1,700), gwanaye ne, daga zuriyar Hebron, su ne suke lura da Isra'ilawan yamma da Urdun a kan aikin Ubangiji da na sarki. 31Yeriya shi ne shugaban zuriyar Hebron bisa ga asalinsu. A shekara ta arba'in ta sarautar Dawuda, sai aka bincika, aka tarar akwai ƙarfafan mutane, jarumawa a cikinsu, a Yazar ta Gileyad. 32Sarki Dawuda ya sa shi, shi da 'yan'uwansu su dubu biyu da ɗari bakwai (2,700) gwanaye, waɗanda suke shugabancin gidajen kakanni, su lura da kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da rabin kabilar Manassa a kan dukan ayyukan Allah da na sarki.

Currently Selected:

1Tar 26: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in