YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 24

24
Ayyukan da aka Raba wa Firistoci
1Ga yadda 'ya'yan Haruna, maza, suka karkasu. 'Ya'yan Haruna, maza, su ne Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar. 2#L.Fir 10.1,2 Amma Nadab da Abihu sun riga mahaifinsu mutuwa, ba su kuma da 'ya'ya. Saboda haka Ele'azara da Itamar suka shiga aikin firistoci. 3Sai Dawuda da Zadok daga zuriyar Ele'azara, da Ahimelek daga zuriyar Itamar suka karkasa su bisa ga ƙayyadaddun lokatansu na yin aiki. 4Tun da yake akwai manyan mutane da yawa a zuriyar Ele'azara fiye da zuriyar Itamar, sai suka karkasa su haka, shugabannin gidajen kakannin zuriyar Ele'azara mutum goma sha shida, na zuriyar Itamar kuwa su takwas, bisa ga gidajen kakanninsu. 5Da haka aka karkasa su ta hanyar kuri'a gama akwai ma'aikatan Wuri Mai Tsarki da kuma ma'aikata na Allah daga zuriyar Ele'azara da zuriyar Itamar. 6Shemaiya, ɗan Netanel marubuci, Balawe, ya rubuta su a gaban sarki da shugabanni, da Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin gidajen kakannin firistoci, da Lawiyawa. Aka ɗauki gida guda daga gidajen kakannin Ele'azara, aka kuma ɗauki ɗaya daga gidajen kakannin Itamar.
7-18Ga yadda aka shirya ƙungiyoyin iyali ashirin da huɗu su sami aikinsu:
1. Yehoyarib
2. Yedaiya
3. Harim
4. Seyorim
5. Malkiya
6. Mijamin
7. Hakkoz
8. Abaija
9. Yeshuwa
10. Shekaniya
11. Eliyashib
12. Yakim
13 Huffa
14. Yeshebeyab
15. Bilga
16. Immer
17. Hezir
18. Haffizzez
19. Fetahiya
20. Yehezkel
21. Yakin
22. Gamul
23. Delaiya
24. Ma'aziya.
19Waɗannan suna da aikin da aka ba su na hidimar Haikalin Ubangiji bisa ga ka'idar da kakansu Haruna ya kafa musu, kamar yadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya umarce shi.
20Sauran 'ya'yan Lawi, maza, na wajen Amram, shi ne Shebuwel.
Na wajen Shebuwel, shi ne Yedaiya.
21Na wajen Rehabiya, shi ne Isshiya,
22Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.
23Na wajen Hebron, su ne Yeriya na fari, da Amariya, da Yahaziyel, da Yekameyam.
24Na wajen Uzziyel, shi ne Mika, na wajen Mika, shi ne Shamir. 25Ɗan'uwan Mika, shi ne Isshiya. Na wajen Isshiya, shi ne Zakariya.
26Na wajen Merari, Mali da Mushi, da Yayaziya. Na wajen Yayaziya, shi ne Beno. 27Na wajen Merari, wato na wajen Yayaziya, su ne Beno, da Shoham, da Zakkur, da Ibri. 28Na wajen Mali, shi ne Ele'azara wanda ba shi da 'ya'ya maza. 29Na wajen Kish, ɗan Kish, shi ne Yerameyel. 30'Ya'yan Mushi, maza, su ne Mali, da Eder, da Yerimot.
Waɗannan su ne 'ya'yan Lawiyawa, maza, bisa ga gidajen kakanninsu.
31Su ma suka jefa kuri'a kamar yadda 'yan'uwansu, 'ya'yan Haruna, maza, suka yi a gaban sarki Dawuda, da Zadok, da Ahimelek, da shugabannin gidajen kakanni na firistoci da na Lawiyawa. Shugaban gidan kakanni ya jefa kuri'a daidai da ƙanensa.

Currently Selected:

1Tar 24: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in