1Tar 2
2
'Ya'yan Isra'ila
(Far 35.22-26)
1Waɗannan su ne 'ya'yan Isra'ila, maza, Ra'ubainu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna, 2da Dan, da Yusufu, da Biliyaminu, da Naftali, da Gad, da Ashiru.
Zuriya Yahuza
3'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela. Waɗannan uku Batshuwa Bakan'aniya, ita ce ta haifa masa su. Amma Er, ɗan farin Yahuza, mugu ne a gaban Ubangiji, don haka Ubangiji ya kashe shi. 4Surukarsa Tamar, matar ɗansa kuma ta haifa masa Feresa da Zera. Yahuza yana da 'ya'ya maza biyar.
5'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul. 6'Ya'yan Zera, maza, su ne Zabdi da Etan, da Heman, da Kalkol, da Darda. Su biyar ke nan. 7#Josh 7.1 Karmi shi ne mahaifin Akan wanda ya jawo wa Isra'ila wahala a kan abin da aka haramta.
8Etan yana da ɗa guda ɗaya, shi ne Azariya.
9'Ya'yan Hesruna, maza, waɗanda aka haifa masa, su ne Yerameyel, da Arama, da kuma Kalibu.
10Arama shi ne mahaifin Amminadab. Amminadab kuma shi ne mahaifin Nashon, shugaban 'ya'yan Yahuza. 11Nashon shi ne mahaifin Salmon. Salmon kuwa shi ne mahaifin Bo'aza. 12Bo'aza kuma shi ne mahaifin Obida. Obida shi ne mahaifin Yesse.
13Yesse shi ne mahaifin Eliyab ɗan farinsa, sa'an nan sai Abinadab da Shimeya, 14da Netanel, da Raddai, 15da Ozem, da Dawuda. Su 'ya'ya maza bakwai ke nan. 16'Yan'uwansu mata kuwa su ne Zeruya da Abigail.
'Ya'yan Zeruya, maza, su ne Abishai, da Yowab, da Asahel, su uku ke nan. 17Abigail ta haifi Amasa. Mahaifin Amasa shi ne Yeter daga zuriyar Isma'ilu.
18Azuba, matar Kalibu ɗan Hesruna ta haifa masa 'ya'ya maza. Matarsa Yeriyot kuma ta haifi 'ya'ya maza, su ne Yesher, da Shobab, da Ardon. 19Sa'ad da Azuba ta rasu sai Kalibu ya auri Efrata wadda ta haifa masa Hur. 20Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuwa shi ne mahaifin Bezalel.
21Bayan haka sai Hesruna ya shiga wurin 'yar Makir mahaifin Gileyad, wadda ya aura sa'ad da yake da shekara sittin da haihuwa. Ta haifa masa Segub. 22Segub shi ne mahaifin Yayir wanda yake da birane ashirin da uku a ƙasar Gileyad. 23Amma sai Geshur da Aram suka ƙwace garuruwan Hawwotyayir ɗin daga gare su, har da Kenat da ƙauyukanta, garuruwa sittin. Duk waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad. 24Bayan rasuwar Hesruna, Abaija, matarsa, ta haifa masa Ashur, mahaifin Tekowa.
25'Ya'yan Yerameyel ɗan farin Hesruna, su ne Arama ɗan fari, sa'an nan Buna, da Oren, da Ozem, da Ahaija. 26Sai Yerameyel ya auro wata mace, sunanta Atara. Ita ce mahaifiyar Onam. 27'Ya'yan Arama, ɗan farin Yerameyel, su ne Ma'az, da Yamin, da Eker. 28'Ya'yan Onam, maza, su ne Shammai da Yada. 'Ya'yan Shammai, maza, su ne Nadab da Abishur.
29Sunan matar Abishur Abihail, ta haifa masa Aban da Molid. 30'Ya'yan Nadab, maza, su ne Seled da Affayim, amma Seled ya rasu bai bar 'ya'ya ba. 31Ɗan Affayim shi ne Ishi. Ɗan Ishi kuwa shi ne Sheshan. Ɗan Sheshan shi ne Alai.
32'Ya'yan Yada, maza, ɗan'uwan Shammai, su ne Yeter da Jonatan. Amma Yeter ya rasu bai bar 'ya'ya ba. 33'Ya'yan Jonatan su ne Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel.
34Sheshan ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Amma yana da wani bara Bamasare mai suna Yarha. 35Sai Sheshan ya aurar wa Yarha baransa da 'yarsa, ita kuwa ta haifar masa Attai. 36Attai shi ne mahaifin Natan, Natan kuma shi ne mahaifin Zabad. 37Zabad kuwa shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne ya haifi Obida. 38Obida shi ne mahaifin Yehu, Yehu kuma shi ne mahaifin Azariya. 39Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa. 40Eleyasa shi ne mahaifin Sisamai, Sisamai shi ne mahaifin Shallum. 41Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya shi ne mahaifin Elishama.
42Ɗan Kalibu, ɗan'uwan Yerameyel, shi ne Mesha ɗan farinsa wanda ya haifi Zif. Zif ya haifi Maresha wanda ya haifi Hebron. 43'Ya'yan Hebron, maza, su ne Kora, da Taffuwa, da Rekem, da Shema. 44Shema shi ne mahaifin Raham wanda ya kafa Yorkeyam. Rekem kuwa shi ne mahaifin Shammai. 45Shammai shi ne mahaifin Mayon, Mayon kuwa shi ne mahaifin Bet-zur.
46Efra ƙwarƙwarar Kalibu, ta haifi Haran, da Moza, da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez.
47'Ya'yan Yadai, maza, su ne Regem, da Yotam, da Geshan, da Felet, da Efa, da Sha'af.
48Ma'aka, ƙwarƙwarar Kalibu, ta haifi Sheber da Tirhana. 49Ta kuma haifi Sha'af mahaifin Madmanna, da Shewa mahaifin Makbena, da mahaifin Gibeya.
'Yar Kalibu ita ce Aksa.
50Waɗannan su ne zuriyar Kalibu, maza.
'Ya'yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, su ne Shobal wanda ya kafa Kiriyat-yeyarim, 51da Salma, shi kuwa ya kafa Baitalami, da Haref ɗansa kuma wanda ya kafa Bet-gader.
52Shobal yana da waɗansu 'ya'ya maza, su ne Rewaiya da wanda yake kakan rabin Manahatiyawa, 53da iyalan da suke a Kiriyat-yeyarim, da na Itiriyawa, da na Futiyawa, da na Shumatiyawa, da na Mishraiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.
54Salma, wanda ya kafa Baitalami, shi ne kakan mutanen Netofa, da na Atarot-bet-yowab, da rabin Manahatiyawa, da Zoratiyawa.
55Iyalan gwanayen rubutu waɗanda suka zauna a Yabez, su ne Tiratiyawa, da Shimeyatiyawa, da Sukatiyawa. Su ne Keniyawa na Hammat, Hammat kuwa shi ne mahaifin mutanen Rekab.
Currently Selected:
1Tar 2: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979