1Tar 1
1
Zuriyar Nuhu
(Far 5.1-32)
1Adamu ya haifi Shitu, Shitu ya haifi Enosh, 2Enosh ya haifi Kenan, Kenan ya haifi Mahalalel, Mahalalel ya haifi Yared, 3Yared ya haifi Anuhu, Anuhu ya haifi Metusela, Metusela ya haifi Lamek. 4Lamek ya haifi Nuhu, Nuhu ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.
Zuriyar Yafet Nuhu
(Far 10.1-32)
5'Ya'yan Yafet, maza ke nan, Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras. 6'Ya'yan Gomer, maza, su ne Ashkenaz, da Rifat, da Togarma. 7'Ya'yan Yawan, maza, su ne Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim.
Zuriyar Ham
(Far 10.6-20)
8'Ya'yan Ham, maza, su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan'ana. 9'Ya'yan Kush, maza, su ne Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra'ama, da Sabteka. 'Ya'yan Ra'ama, maza, su ne Sheba da Dedan. 10Kush shi ne mahaifin Lamirudu wanda shi ne ya fara ƙasaita a duniya. 11Mizrayim shi ne mahaifin jama'ar Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Naftuhawa, 12da Fatrusawa, da Kasluhawa tushen Filistiyawa ke nan, da Kaftorawa. 13Kan'ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Het, 14da Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa, 15da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa, 16da Arwadiyawa, da Zemariyawa, da Hamatiyawa.
Zuriyar Shem
(Far 11.10-26)
17'Ya'yan Shem, maza, su ne Elam, da Asshur, da Arfakshad, da Lud, da Aram, da Uz, da Hul, da Geter, da Meshek. 18Arfakshad shi ne mahaifin Shela, Shela kuma shi ne mahaifin Eber. 19'Ya'ya biyu maza ne aka haifa wa Eber. Sunan ɗayan Feleg, saboda a lokacinsa ne aka karkasa duniya, sunan ɗan'uwansa kuwa Yokatan. 20Yokatan shi ne mahaifin Almoda, da Shelef, da Hazarmawet, da Yera, 21da Adoniram, da Uzal, da Dikla, 22da Ebal, da Abimayel, da Sheba, 23da Ofir, da Hawila, da Yobab. Waɗannan duka su ne 'ya'yan Yokatan, maza.
24Shem ya haifi Arfakshad, Arfakshad ya haifi Shela, 25Shela ya haifi Eber, Eber ya haifi Feleg, Feleg ya haifi Reyu, 26Reyu ya haifi Serug, Serug ya haifi Nahor, Nahor ya haifi Tera, 27Tera ya haifi Abram, wato Ibrahim ke nan.
Zuriyar Isma'ilu da Ketura
(Far 25.1-4,12-16)
28'Ya'yan Ibrahim, maza, su ne Ishaku da Isma'ilu. 29Ga zuriyarsu. Nabayot shi ne ɗan farin Isma'ilu, sa'an nan sai Kedar, da Abdeyel, da Mibsam, 30da Mishma, da Duma, da Massa, da Hadad, da Tema, 31da Yetur, da Nafish, da Kedema. Waɗannan su ne 'ya'yan Isma'ilu, maza.
32'Ya'ya maza na Ketura, wato ƙwarƙwarar Ibrahim, su ne Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa. 'Ya'yan Yokshan, maza, su ne Sheba, da Dedan. 33'Ya'yan Madayana, maza, su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka su ne 'ya'yan Ketura, maza.
Zuriyar Isuwa
(Far 36.1-43)
34Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. 'Ya'yan Ishaku, maza, su ne Isuwa da Isra'ila. 35'Ya'yan Isuwa, maza, su ne Elifaz, da Reyuwel, da Yewush, da Yalam da Kora. 36'Ya'yan Elifaz, maza, su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz, da Tima, da Amalek. 37'Ya'yan Reyuwel, maza kuwa, su ne Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza.
38'Ya'yan Seyir, maza kuma, su ne Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana, da Dishon, da Ezer, da kuma Dishan.
39'Ya'yan Lotan, maza, su ne Hori, da Hemam. Timna ce 'yar'uwar Lotan.
40'Ya'yan Shobal, maza, su ne Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam.
'Ya'yan Zibeyon, maza su ne Aiya da Ana. 41Dishon shi ne ɗan Ana. 'Ya'yan Dishon, maza kuwa, su ne Hemdan, da Eshban, da Yitran, da Keran.
42'Ya'yan Ezer, maza, su ne Bilhan, da Zayawan, da Akan. 'Ya'yan Dishan, maza, su ne Uz da Aran.
43-50Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom kafin wani Sarkin Isra'ila ya ci sarauta.
Bela ɗan Beyor, sunan birninsa kuwa Dinhaba
Yobab ɗan Zera na Bozara
Husham na ƙasar Teman
Hadad ɗan Bedad na Awit, wanda ya kori Madayanawa a filin Mowab
Samla na Masrek
Shawul na Rehobot wadda take bakin Kogin Yufiretis
Ba'al-hanan ɗan Akbor
Hadad na Fau, sunan matarsa kuma Mehetabel 'yar Matred, wato jikar Mezahab.
51Hadad kuwa ya rasu. Sarakunan Edom su ne Timna, da Alwa, da Yetet, 52da Oholibama, da Ila, da Finon, 53da Kenaz, da Teman, da Mibzar, 54da Magdiyel, da Iram.
Currently Selected:
1Tar 1: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979