YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 3

3
'Ya'yan Dawuda
(2Sam 3.2-5; 5.13-16; 1Tar 14.3-7)
1-3 # 1Tar 14.3; 28.5; Josh 15.56; 1Sam 25.42; 1Sar 2.22 Waɗannan su ne 'ya'yan Dawuda, maza, waɗanda aka haifa masa a Hebron.
Amnon wanda Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa.
Kileyab wanda Abigail Bakarmeliya ta haifa masa.
Absalom ɗan Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur.
Adonaija ɗan Haggit.
Shefatiya wanda Abital ta haifa.
Itireyam wanda Egla ta haifa.
4 # 2Sam 5.4; 1Tar 29.27; 2Sam 2.11; 5.5 Dukansu shida an haife su ne a Hebron inda ya yi sarauta shekara bakwai da wata shida.
Ya yi sarauta a Urushalima shekara talatin da uku. 5#2Sam 11.3; 12.24 Waɗanda aka haifa masa a Urushalima, su ne Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, su huɗu ke nan waɗanda Bat-sheba 'yar Ammiyel ta haifa masa.
6Yana da waɗansu 'ya'ya kuma, su ne Ibhar, da Elishuwa da Elifelet, 7da Noga, da Nefeg, da Yafiya, 8da Elishama, da Eliyada, da kuma Elifelet, su tara ke nan. 9#2Sam 13.1; 1Tar 14.4 Waɗannan duka su ne 'ya'yan Dawuda, maza, banda 'ya'yan ƙwaraƙwarai. Tamar ita ce 'yar'uwarsu.
Zuriyar Sulemanu
10 # 1Sar 11.43; 14.21-31; 2Tar 12.16; 2Tar 17.1—21.3 Waɗannan su ne zuriyar Sulemanu, daga Rehobowam, sai Abaija, da Asa, da Yehoshafat, 11#2Sar 8.16-24; 2Tar 21.1; 2Tar 22.1-10; 2Sar 11.1—12.21 da Yoram, da Ahaziya, da Yowash, 12#2Sar 14.1-22; 2Tar 25.1-28; Ish 1.1; Yush 1.1; Mika 1.1 da Amaziya, da Azariya, da Yotam, 13#2Sar 16.1-20; 2Tar 28.1; Ish 7.1; 2Sar 18.1—20.21; 2Tar 29.1; Irm 26.19; 2Tar 33.1 da Ahaz, da Hezekiya da Manassa, 14#2Sar 21.19-26; 2Tar 33.21; Zaf 1.1; 2Tar 34.1; Irm 1.2; 3.6; 25.3 da Amon, da Yosiya. 15#2Sar 23.34; Irm 37.1; 2Sar 23.31 'Ya'yan Yosiya, maza, su ne Yohenan ɗan farinsa, na biyu shi ne Eliyakim, na uku shi ne Zadakiya, na huɗu shi ne Yehowahaz, 16#2Sar 24.6,8; Mat 1.11; 2Sar 24.18 Eliyakim yana da 'ya'ya biyu maza, su ne Yekoniya, da Zadakiya.
17 # Ezra 3.2 'Ya'yan Yekoniya wanda aka kama, su ne Sheyaltiyel, 18#Ezra 1.8; 5.14; Irm 22.30 da Malkiram, da Fedaiya, da Shenazzar, da Yekamiya, da Hoshama, da Nedabiya. 19#Ezra 2.2; 3.2; 5.2; Neh 7.7; 12.1; Hag 1.1; 2.2; Zak 4.6 Fedaiya yana da 'ya'ya biyu maza, su ne Zarubabel da Shimai. 'Ya'yan Zarubabel, maza, su ne Meshullam, da Hananiya, da Shelomit 'yar'uwarsu, 20da Hashuba, da Ohel, da Berikiya, da Hasadiya, da Yushab-hesed, su biyar ke nan.
21'Ya'yan Hananiya, maza, su ne Felatiya, da Yeshaya, da 'ya'yan Refaya, maza, da 'ya'yan Arnan, maza, da 'ya'yan Obadiya, maza, da 'ya'yan Shekaniya, maza. 22#Ezra 8.2-3 Ɗan Shekaniya shi ne Shemaiya. 'Ya'yan Shemaiya, maza, su ne Hattush, da Igal, da Bariya da Neyariya, da Shafat, su shida ke nan. 23'Ya'yan Neyariya, maza, su ne Eliyehoyenai, da Hezekiya, da Azrikam, su uku ne nan. 24'Ya'yan Eliyehoyenai, maza, su ne Hodawiya, da Eliyashib, da Felaya, da Akkub, da Yohenan, da Dalaya, da Anani, su bakwai ke nan.

Currently Selected:

1Tar 3: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in