YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 16

16
1Suka fa shigo da akwatin alkawarin Allah, suka ajiye shi a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa masa, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama a gaban Allah. 2Da Dawuda ya gama miƙa hadayar ƙonawa da ta salama, sai ya sa wa jama'a albarka da sunan Ubangiji. 3Ya kuma rarraba wa Isra'ilawa mata da maza, gurasa, da gunduwar nama, da kauɗar zabibi.
4Ya kuma sa waɗansu Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka Ubangiji Allah na Isra'ila, su gode masa, su kuma yabe shi. 5Asaf shi ne shugaba, na biye da shi su ne Zakariya da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Mattitiya, da Eliyab, da Benaiya, da Obed-edom, da Yehiyel, waɗanda za su kaɗa molaye da garayu. Asaf kuwa shi ne mai kaɗa kuge. 6Benaiya da Yahaziyel firistoci, su ne za su riƙa busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah.
Waƙar Yabo ta Dawuda
(Zab 105.1-15; 96.1-13; 106.47-48)
7A wannan lokaci ne Dawuda ya fara sa Asaf da 'yan'uwansa su riƙa raira waƙoƙin yabo ga Ubangiji.
8Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa,
Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!
9Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi,
Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!
10Ku yi murna saboda mu nasa ne,
Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!
11Ku je wurin Ubangiji neman taimako,
Ku tsaya a gabansa koyaushe.
12Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki,
Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.
13Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,
Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu.
14Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,
Umarnansa domin dukan duniya ne.
15Zai cika alkawarinsa har abada,
Alkawaransa kuma don dubban zamanai,
16 # Far 12.7; Far 26.3 Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim,
Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.
17 # Far 28.13 Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra'ila,
Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa'ad da ya ce,
18“Zan ba ka ƙasar Kan'ana,
Za ta zama mallakarka.”
19Jama'ar Ubangiji kima ne,
Baƙi ne kuwa a ƙasar.
20Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa,
Daga wannan mulki zuwa wancan.
21 # Far 20.3-7 Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba,
Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.
22Ya ce, “Kada ku taɓa bayina, zaɓaɓɓu,
Kada ku cuci annabawana!”
23Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku dukan duniya,
Ku yi shelar albishir na ceton da ya yi mana kowace rana.
24Ku yi shelar ɗaukakarsa ga al'ummai,
Da ayyukansa masu girma ga dukan mutane,
25Ubangiji da girma yake, wajibi ne mu yabe shi,
Dole mu yi tsoronsa fiye da dukan alloli.
26Gama allolin dukan sauran al'umma gumaka ne,
Amma Ubangiji shi ne ya halitta sammai.
27Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,
Iko da farin ciki sun cika haikalinsa.
28Ku yi yabon Ubangiji, ku dukan mutanen duniya,
Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!
29Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja,
Kuna kawo sadaka, kuna zuwa Haikalinsa.
Ku rusuna a gaban Mai Tsarki da sahihiyar zuciya,
30Ku yi rawar jiki a gabansa, ku dukan duniya!
Hakika duniya ta kahu sosai, ba za ta jijjigu ba.
31Duniya da sararin sama, ku yi farin ciki!
Ku faɗa wa al'ummai, Ubangiji shi ne sarki.
32Ki yi ruri, ke teku, da dukan abin da yake cikinki,
Ka yi farin ciki, kai saura da dukan abin da yake cikinka.
33Itatuwa a jeji za su yi sowa domin murna
Sa'ad da Ubangiji zai zo ya yi mulki a duniya.
34 # 2Tar 5.13; 7.3; Ezra 3.11; Zab 100.5; 106.1; 107.1; 118.1; 136.1; Irm 33.11 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne,
Ƙaunarsa madawwamiya ce!
35Ku ce masa, “Ka cece mu, ya Allah Mai Cetonmu,
Ka tattara mu, ka kuɓutar da mu daga al'ummai,
Domin mu gode maka,
Mu kuma yabi sunanka mai tsarki.”
36Ku yabi Ubangiji Allah na Isra'ila!
Ku yi ta yabonsa har abada abadin!
Sa'an nan dukan jama'a suka ce, “Amin, Amin,” suka yabi Ubangiji.
An Zaɓi Lawiyawa domin Akwatin Alkawari
37Dawuda ya sa Asaf tare da 'yan'uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji domin a yi hidima kullayaumin a gaban akwatin alkawarin kamar yadda aka bukaci a yi kowace rana. 38Akwai kuma masu tsaron ƙofofi, wato Obed-edom ɗan Yedutun tare da 'yan'uwansa, su sittin da takwas, da Hosa.
39Sai ya bar Zadok firist da 'yan'uwansa firistoci a wurin zama na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon. 40Kowace safiya da maraice suna miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a bisa bagaden ƙona hadaya, kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, waɗanda ya ba Isra'ilawa. 41Tare da su kuma akwai Heman, da Yedutun, da sauran waɗanda aka zaɓa musamman domin su yi godiya ga Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa. 42Heman da Yedutun suna lura da ƙaho, da kuge, da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin raira waƙoƙin yabo ga Allah. 'Ya'yan Yedutun, maza, su aka ba aikin tsaron ƙofa.
43 # 2Sam 6.19,20 Sa'an nan dukan jama'a suka watse, kowa ya koma gidansa, Dawuda kuma ya koma gidansa, ya sa wa iyalinsa albarka.

Currently Selected:

1Tar 16: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in