1
1Tar 16:11
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ku je wurin Ubangiji neman taimako, Ku tsaya a gabansa koyaushe.
Compare
Explore 1Tar 16:11
2
1Tar 16:34
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce!
Explore 1Tar 16:34
3
1Tar 16:8
Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa, Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!
Explore 1Tar 16:8
4
1Tar 16:10
Ku yi murna saboda mu nasa ne, Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!
Explore 1Tar 16:10
5
1Tar 16:12
Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki, Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.
Explore 1Tar 16:12
6
1Tar 16:9
Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi, Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!
Explore 1Tar 16:9
7
1Tar 16:25
Ubangiji da girma yake, wajibi ne mu yabe shi, Dole mu yi tsoronsa fiye da dukan alloli.
Explore 1Tar 16:25
8
1Tar 16:29
Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja, Kuna kawo sadaka, kuna zuwa Haikalinsa. Ku rusuna a gaban Mai Tsarki da sahihiyar zuciya
Explore 1Tar 16:29
9
1Tar 16:27
Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi, Iko da farin ciki sun cika haikalinsa.
Explore 1Tar 16:27
10
1Tar 16:23
Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku dukan duniya, Ku yi shelar albishir na ceton da ya yi mana kowace rana.
Explore 1Tar 16:23
11
1Tar 16:24
Ku yi shelar ɗaukakarsa ga al'ummai, Da ayyukansa masu girma ga dukan mutane
Explore 1Tar 16:24
12
1Tar 16:22
Ya ce, “Kada ku taɓa bayina, zaɓaɓɓu, Kada ku cuci annabawana!”
Explore 1Tar 16:22
13
1Tar 16:26
Gama allolin dukan sauran al'umma gumaka ne, Amma Ubangiji shi ne ya halitta sammai.
Explore 1Tar 16:26
14
1Tar 16:15
Zai cika alkawarinsa har abada, Alkawaransa kuma don dubban zamanai
Explore 1Tar 16:15
15
1Tar 16:31
Duniya da sararin sama, ku yi farin ciki! Ku faɗa wa al'ummai, Ubangiji shi ne sarki.
Explore 1Tar 16:31
16
1Tar 16:36
Ku yabi Ubangiji Allah na Isra'ila! Ku yi ta yabonsa har abada abadin! Sa'an nan dukan jama'a suka ce, “Amin, Amin,” suka yabi Ubangiji.
Explore 1Tar 16:36
17
1Tar 16:28
Ku yi yabon Ubangiji, ku dukan mutanen duniya, Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!
Explore 1Tar 16:28