YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 15

15
An Kawo Akwatin Alkawari a Urushalima
(2Sam 6.12-23)
1Dawuda kuwa ya gina wa kansa gidaje a birninsa, ya kuma kafa alfarwa domin akwatin alkawari na Allah. 2#M.Sh 10.8 Sai Dawuda ya ce, “Kada wani ya ɗauki akwatin alkawari na Allah sai Lawiyawa kaɗai, gama su ne Ubangiji ya zaɓa domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su kuma yi masa hidima har abada.” 3Saboda haka Dawuda ya tattara Isra'ilawa duka a Urushalima don a kawo akwatin alkawarin Ubangiji a wurinsa, inda aka riga aka shirya masa. 4Dawuda kuma ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya, tare kuma da Lawiyawa. 5Waɗanda aka tattaro ke nan, daga iyalin Kohat su ɗari da shirin ne. Uriyel shi ne shugabansu. 6Daga iyalin Merari su ɗari biyu da ashirin, Asaya ne shugabansu. 7Daga iyalin Gershon ɗari da talatin, Yowel ne shugabansu. 8Daga iyalin Elizafan ɗari biyu, Shemaiya ne shugabansu. 9Daga iyalin Hebron su tamanin, Eliyel ne shugabansu. 10Daga iyalin Uzziyel ɗari da goma sha biyu, Amminadab ne shugabansu.
11Sa'an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyata firistoci, da Lawiyawa, wato Uriyel, da Asaya, da Yowel, da Shemaiya, da Eliyel, da Amminadab, 12ya ce musu, “Ku ne shugabanni na gidajen kakanninku, Lawiyawa. Sai ku tsarkake kanku da 'yan'uwanku domin ku iya kawo akwatin alkawarin Allah na Isra'ila a inda na shirya masa. 13Gama Ubangiji Allahnmu ya fashe fushinsa a kanmu saboda ba ku ne kuka ɗauke shi a karo na farko ba, saboda kuma ba mu yi masa sujada kamar yadda aka umarta ba.”
14Sa'an nan firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji Allah na Isra'ila. 15#Fit 25.14 Lawiyawa fa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah a bisa sandunansa a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.
16Dawuda ya umarci shugabannin Lawiyawa su sa 'yan'uwansu mawaƙa su riƙa raira waƙa da murna, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, da molaye, da garayu, da kuge masu amon gaske. 17Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berikiya daga cikin 'yan'uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kishi. 18Daga cikin 'yan'uwansu, har yanzu aka zaɓi mataimakansu, wato Zakariya, da Ben, da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Unno, da Eliyab, da Benaiya, da Ma'aseya, da Mattitiya, da Elifelehu, da Mikneya, da Obed-edom, da Yehiyel, da masu tsaron ƙofofi.
19Haka aka zaɓi mawaƙa, wato Heman, da Asaf, da Etan don su buga kuge na tagulla. 20Su Zakariya, da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Unno, da Eliyab, da Ma'aseya, da Benaiya, su ne masu kaɗa molaye da murya a sama.
21Su Mattitiya, da Elifelehu, da Mikneya, da Obed-edom, da Yehiyel, da Azaziya suke ja da garayu da murya ƙasa-ƙasa.
22Kenaniya shugaban Lawiyawa shi ne yake bi da waƙoƙi domin shi gwani ne. 23Berikiya da Elkana su ne masu tsaron ƙofa ta akwatin alkawari. 24Sai Shebaniya, da Yehoshafat, da Netanel, da Amasai, da Zakariya, da Benaiya, da Eliyezer, firistoci, suka yi ta busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-edom da Yehiya su ne kuma masu tsaron ƙofar akwatin alkawari.
25Haka Dawuda, da dattawan Isra'ilawa, da shugabannin dubu dubu, suka tafi da murna domin su ɗauko akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-edom. 26Saboda Allah ya taimaki Lawiyawa waɗanda suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi hadaya da bijimai bakwai da raguna bakwai. 27Dawuda yana saye da kyakkyawar taguwa ta lilin tare da Lawiyawa duka waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, da mawaƙa, da Kenaniya shugaban mawaƙan. Dawuda kuma ya sa falmaran ta lilin. 28Da haka fa Isra'ilawa duka suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suna ta sowa, suna ta busa ƙaho, suna kaɗa kuge da molaye, da garayu.
29Sa'ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shigo birnin Dawuda, sai Mikal 'yar Saul ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana ta rawa, yana murna, sai ta ji ya saƙale mata a zuci.

Currently Selected:

1Tar 15: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in