1Tar 14
14
Hiram da Dawuda
(2Sam 5.11-12)
1Sai Hiram Sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda, su kai masa itatuwan al'ul, da magina, da massassaƙa domin a gina masa fāda. 2Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya tabbatar masa da sarautar Isra'ila, mulkinsa kuwa ya ɗaukaka ƙwarai saboda jama'arsa, Isra'ila.
'Ya'yan da aka Haifa wa Dawuda a Urushalima
(2Sam 5.13-16; 1Tar 3.5-9)
3Dawuda kuwa ya ƙara auren waɗansu mata a Urushalima, suka haifi 'ya'ya mata da maza. 4Ga sunayen 'ya'yan da aka haifa masa a Urushalima, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, 5da Ibhar, da Elishuwa, da Elifelet, 6da Noga, da Nefeg, da Yafiya, 7da Elishama, da Eliyada, da Elifelet.
Dawuda Ya Ci Filistiyawa da Yaƙi
(2Sam 5.17-25)
8Sa'ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila duka, sai dukan Filistiyawa suka haura, suna neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya fita domin ya yi yaƙi da su. 9Filistiyawa suka iso kwarin Refayawa suka fara fatali da shi. 10Sai Dawuda ya roƙi Allah, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?”
Ubangiji kuwa ya amsa masa, ya ce, “Ka haura, gama zan bashe su a hannunka.”
11Sai suka haura zuwa Ba'al-ferazim, Dawuda kuwa ya ci su da yaƙi a wurin. Sai ya ce, “Allah ya raraki maƙiyana ta hannuna, kamar yadda ruwa yakan rarake ƙasa.” Don haka aka sa wa wurin suna Ba'al-ferazim. 12Filistiyawa suka gudu suka bar gumakansu a wurin. Dawuda kuwa ya yi umarni, aka ƙone su duka.
13Filistiyawa kuma suka sāke kawo yaƙi a kwarin. 14Dawuda ya sāke yin roƙo ga Allah, Allah kuwa ya ce masa, “Kada ka hau zuwa wurinsu, ka kewaye ka ɓullo musu ta baya daura da itatuwan tsamiya. 15Sa'ad da ka ji motsi kamar na tafiyar sojoji a bisa itatuwan tsamiya, sai ka fita ka yi yaƙi, gama Allah ya wuce ta gabanka don ya bugi sojojin Filistiyawa.” 16Dawuda fa ya yi daidai yadda Ubangiji ya umarce shi. Suka bugi sojojin Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer. 17Sunan Dawuda kuma ya kai ko'ina cikin dukan ƙasashe. Ubangiji kuwa ya sa dukan al'ummai su ji tsoron Dawuda.
Currently Selected:
1Tar 14: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979