Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?” Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce musu, su dai huta kaɗan, har a cika adadin abokan bautarsu, wato, 'yan'uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.