1
Zab 77:11-12
Littafi Mai Tsarki
HAU
Zan tuna da manyan ayyukanka, ya Ubangiji, Zan tuna da al'amura masu banmamaki da ka aikata a dā. Zan tuna da dukan abubuwan da ka yi, Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka.
Compare
Explore Zab 77:11-12
2
Zab 77:14
Kai ne Allah wanda kake aikata al'ajabai, Ka nuna ikonka cikin sauran al'umma.
Explore Zab 77:14
3
Zab 77:13
Dukan abin da kake yi mai tsarki ne, ya Allah! Ba wani allah mai girma kamarka!
Explore Zab 77:13
4
Zab 77:1-2
Na ta da murya, na yi kuka ga Allah, Na ta da murya, na yi kuka, ya kuwa ji ni. A lokacin wahala, nakan yi addu'a ga Ubangiji, Dukan dare nakan ɗaga hannuwana sama in yi addu'a, Amma ban sami ta'aziyya ba.
Explore Zab 77:1-2