Bible App logo
Search Icon

Zab 77

77
Ta'aziyya a Lokacin Damuwa
1Na ta da murya, na yi kuka ga Allah,
Na ta da murya, na yi kuka, ya kuwa ji ni.
2A lokacin wahala, nakan yi addu'a ga Ubangiji,
Dukan dare nakan ɗaga hannuwana sama in yi addu'a,
Amma ban sami ta'aziyya ba.
3Lokacin da na tuna da Allah na yi ajiyar zuciya.
Sa'ad da nake tunani,
Nakan ji kamar in fid da zuciya.
4Ba ya barina in yi barci,
Na damu har na kāsa magana.
5Na yi tunanin kwanakin da suka wuce,
Nakan kuma tuna da shekarun da suka wuce da daɗewa.
6Dare farai ina ta tunani mai zurfi,
A cikin tunani nakan yi wa kaina tambaya.
7A kullum ne Ubangiji zai yashe ni?
Ba kuma zai ƙara yin murna da ni ba?
8Ya daina ƙaunata ke nan?
Alkawarinsa ba shi da wani amfani?
9Allah ya manta da yin jinƙai ne?
Fushinsa ya maye matsayin juyayinsa ne?
10Sa'an nan sai na ce, “Abin da ya fi mini zafi duka,
Shi ne ikon Maɗaukaki ya ragu.”
11Zan tuna da manyan ayyukanka, ya Ubangiji,
Zan tuna da al'amura masu banmamaki da ka aikata a dā.
12Zan tuna da dukan abubuwan da ka yi,
Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka.
13Dukan abin da kake yi mai tsarki ne, ya Allah!
Ba wani allah mai girma kamarka!
14Kai ne Allah wanda kake aikata al'ajabai,
Ka nuna ikonka cikin sauran al'umma.
15Ta wurin ikonka ka fanshi jama'arka,
Zuriyar Yakubu da ta Yusufu.
16Ya Allah, sa'ad da ruwaye suka gan ka, sai su tsorata,
Zurfafan teku kuma suka yi rawar jiki.
17Gizagizai suka zubo da ruwa,
Aka buga tsawa daga sama,
Aka kuwa yi walƙiya ko'ina.
18Bugawar tsawarka ta gama ko'ina,
Hasken walƙiya ya haskaka dukan duniya,
Duniya ta yi rawa, ta girgiza, ta kaɗu.
19Ka yi tafiya a teku,
Ka haye teku mai zurfi,
Amma ba a ga shaida inda ka taka ba.
20Ka bi da jama'arka yadda makiyayi yake yi,
Musa da Haruna suke lura da su.

Currently Selected:

Zab 77: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for Zab 77