1
K.Mag 12:25
Littafi Mai Tsarki
HAU
Damuwa takan hana wa mutum farin ciki, amma kalmomin alheri za su sa shi ya yi murna.
Compare
Explore K.Mag 12:25
2
K.Mag 12:1
Mutumin da yake ƙaunar ilimi yakan so a faɗa masa kuskurensa, wauta ce mutum ya ƙi yarda a faɗa masa laifinsa.
Explore K.Mag 12:1
3
K.Mag 12:18
Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka.
Explore K.Mag 12:18
4
K.Mag 12:15
Wawa a kullum tsammani yake abin da yake yi daidai ne, amma masu hikima sukan kasa kunne ga shawara.
Explore K.Mag 12:15
5
K.Mag 12:16
Sa'ad da wawa ya hasala, nan da nan kowa zai sani, amma mai la'akari ba zai nuna ya kula ba.
Explore K.Mag 12:16
6
K.Mag 12:4
Matar kirki abar fāriya ce, abar murna ga mijinta, amma idan ta sa shi kunya, ta zama masa kamar ciwo a ƙashinsa.
Explore K.Mag 12:4
7
K.Mag 12:22
Ubangiji yana ƙin maƙaryata, amma yana murna da masu faɗa da cikawa.
Explore K.Mag 12:22
8
K.Mag 12:26
A ko yaushe adalin mutum yakan gwada halinsa, amma mugaye sukan ɓata a hanya.
Explore K.Mag 12:26
9
K.Mag 12:19
Gaskiya dawwamammiya ce, amma ƙarya ƙurarriya ce.
Explore K.Mag 12:19
Home
Bible
Plans
Videos