“Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanaki
suna zuwa,
Sa'ad da zan tsiro da wani mai adalci
daga zuriyar Dawuda
Wanda zai ci sarauta.
Zai yi sarauta da hikima,
Zai aikata abin da yake daidai a
ƙasar.
A zamaninsa za a ceci Yahuza,
Isra'ila kuwa za ta zauna lafiya.
Sunan da za a kira shi da shi ke
nan,
‘Ubangiji Adalcinmu.’