1
Ish 54:17
Littafi Mai Tsarki
HAU
Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki, Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki. Zan kāre bayina, In kuwa ba su nasara.” Ubangiji ne ya faɗa.
Compare
Explore Ish 54:17
2
Ish 54:10
Duwatsu da tuddai za su ragargaje, Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam. Zan cika alkawarina na salama har abada.” Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.
Explore Ish 54:10
3
Ish 54:4
Kada ki ji tsoro, ba za a ƙara kunyatar da ke ba, Ba kuwa za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da rashin amincinki irin na matar ƙuruciya, Za ki manta da matsanancin kaɗaicinki, Mai kama da na gwauruwa.
Explore Ish 54:4
4
Ish 54:5
Mahaliccinki zai zama kamar miji a gare ki, Sunansa Ubangiji Mai Runduna! Allah Mai Tsarki na Isra'ila mai fansarki ne, Shi ne mai mulkin dukan duniya!
Explore Ish 54:5
5
Ish 54:2
Ki fāɗaɗa alfarwar da kike zama ciki! Ki ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta!
Explore Ish 54:2
6
Ish 54:13
“Ni kaina zan koya wa mutanenki, Zan kuwa ba su wadata da salama.
Explore Ish 54:13
7
Ish 54:8
Na juya, na rabu da ke da fushi na ɗan lokaci, Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.” Haka Ubangiji mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.
Explore Ish 54:8
8
Ish 54:7
“A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.
Explore Ish 54:7
9
Ish 54:9
“Na yi alkawari a zamanin Nuhu, Cewa ba zan ƙara rufe duniya da Ruwan Tsufana ba. Yanzu kuwa ina miki alkawari, Cewa ba zan ƙara yin fushi da ke ba, Ba zan ƙara tsawata miki, ko in hukunta ki ba.
Explore Ish 54:9
10
Ish 54:12
Zan gina hasumiyarki da jan yakutu, Da ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske kamar hasken wuta, Da garun da ya kewaye ki kuwa zan gina ta da lu'ulu'ai.
Explore Ish 54:12
Home
Bible
Plans
Videos