1
Ish 43:19
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ku duba abin da nake shirin yi. Yana ta faruwa ma, kuna iya ganinsa yanzu! Zan yi hanya a cikin jeji, In kuma ba ku rafuffukan ruwa a can.
Compare
Explore Ish 43:19
2
Ish 43:2
Sa'ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi, Zan kasance tare da ku, Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba. Sa'ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba, Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.
Explore Ish 43:2
3
Ish 43:18
Amma Ubangiji ya ce, “Kada ku maƙale wa abubuwan da suka wuce, Ko ku riƙa tunanin abin da ya faru tuntuni.
Explore Ish 43:18
4
Ish 43:1
Ya Isra'ila, Ubangiji wanda ya halicce ku ya ce, “Kada ku ji tsoro, na fanshe ku. Na kira ku da sunanku, ku nawa ne.
Explore Ish 43:1
5
Ish 43:4
Zan ba da dukan al'ummai don in ceci ranku, Gama kuna da daraja a gare ni, Gama na ba ku girma, ina kuma ƙaunarku.
Explore Ish 43:4
6
Ish 43:3
Gama ni ne Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, wanda ya cece ku. Zan ba da Masar, da Habasha, da Seba Ga Sairus domin fansarku.
Explore Ish 43:3
7
Ish 43:5
Kada ku ji tsoro, ina tare da ku! “Daga gabas mafi nisa, da kuma yamma mafi nisa, Zan kawo jama'arku zuwa gida.
Explore Ish 43:5
8
Ish 43:25
Duk da haka, ni ne Allah wanda ya shafe zunubanku, Na kuwa yi haka saboda yadda nake. Ba zan ƙara tunawa da zunubanku kuma ba.
Explore Ish 43:25
9
Ish 43:10
“Ya jama'ar Isra'ila, ku ne shaiduna, Na zaɓe ku al'umma, baiwata, Domin ku san ni, ku gaskata ni, Ku kuma fahimta, ni kaɗai ne Allah. In banda ni ba wani Allah, Ba a taɓa yin wani ba, Ba kuwa za a yi ba.
Explore Ish 43:10
10
Ish 43:11
“Ni kaɗai ne Ubangiji, Ni kaɗai ne wanda yake da ikon yin ceto.
Explore Ish 43:11
11
Ish 43:13
Ni ne Allah, haka kuwa nake tutur, Ba wanda zai iya tserewa daga ikona, Ba mai iya sāke abin da na riga na yi.”
Explore Ish 43:13
12
Ish 43:20-21
Har da namomin jeji za su girmama ni, Diloli da jiminai za su yi yabona Sa'ad da na sa kogunan ruwa su yi gudu a hamada, Domin su ba da ruwa ga zaɓaɓɓun mutanena. Su ne mutanen da na yi domin kaina, Za su raira yabbaina!”
Explore Ish 43:20-21
13
Ish 43:6-7
Zan faɗa wa kudu su bar su su tafi, Arewa kuma kada su riƙe su a can. Bari mutanena su komo daga manisantan ƙasashe, Daga kowane sashi na duniya. Su mutanena ne, na kaina, Na kuwa halicce su don su girmama ni.”
Explore Ish 43:6-7
14
Ish 43:16-17
Tuntuni Ubangiji ya shirya hanya ta cikin teku, Da turba kuma a cikin ruwa. Ya bi da manyan sojoji zuwa hallaka, Sojojin karusai da na dawakai. Sun faɗi warwar, ba za su ƙara tashi ba, An hure su kamar 'yar wutar fitila!
Explore Ish 43:16-17
15
Ish 43:15
Ni ne Ubangiji, Allahnku Mai Tsarki na Isra'ila, Ni na halicce ku, ni ne kuma sarkinku.”
Explore Ish 43:15
Home
Bible
Plans
Videos