1
Ish 42:6-7
Littafi Mai Tsarki
HAU
“Ni Ubangiji, na kira ka, na kuma ba ka iko Domin ka ga ana aikata gaskiya a duniya. Ta wurinka zan yi wa dukan mutane alkawari, Ta wurinka zan kawo haske ga al'ummai. Za ka buɗe idanun makafi, Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.
Compare
Explore Ish 42:6-7
2
Ish 42:8
“Ni kaɗai ne Ubangiji Allahnka. Ba wani allahn da zai sami ɗaukakata, Ba zan bar gumaka su sami yabona ba.
Explore Ish 42:8
3
Ish 42:1
Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.
Explore Ish 42:1
4
Ish 42:3-4
Zai lallaɓi marasa ƙarfi, Ya nuna alheri ga tafkakku. Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka. Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba, Zai kuma kafa gaskiya a duniya, Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”
Explore Ish 42:3-4
5
Ish 42:16
“Zan yi wa mutanena makafi jagora A hanyar da ba su taɓa bi ba. Zan sa duhunsu ya zama haske, In kuma sa ƙasa mai kururrumai ta zama sumul a gabansu. Ba zan kasa yin waɗannan abu ba.
Explore Ish 42:16
6
Ish 42:9
Abubuwan da na faɗa yanzu sun cika. Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwa, Tun kafin ma su soma faruwa.”
Explore Ish 42:9
Home
Bible
Plans
Videos