Ish 43:16-17
Ish 43:16-17 HAU
Tuntuni Ubangiji ya shirya hanya ta cikin teku, Da turba kuma a cikin ruwa. Ya bi da manyan sojoji zuwa hallaka, Sojojin karusai da na dawakai. Sun faɗi warwar, ba za su ƙara tashi ba, An hure su kamar 'yar wutar fitila!





