Ko da yake itacen ɓaure bai yi toho ba,
Ba kuma 'ya'ya a kurangar inabi,
Zaitun kuma bai ba da amfani ba,
Gonaki ba su ba da abinci ba,
An kuma raba garken tumaki daga cikin garke,
Ba kuma shanu a turaku,
Duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,
Zan yi murna da Allah Mai Cetona.