Hab 3:17-18
Hab 3:17-18 HAU
Ko da yake itacen ɓaure bai yi toho ba, Ba kuma 'ya'ya a kurangar inabi, Zaitun kuma bai ba da amfani ba, Gonaki ba su ba da abinci ba, An kuma raba garken tumaki daga cikin garke, Ba kuma shanu a turaku, Duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, Zan yi murna da Allah Mai Cetona.








