Sai Ubangiji ya ce mini,
“Ka rubuta wahayin da kyau a kan alluna,
Yadda kowa zai karanta shi a sawwaƙe.
Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa,
Yana gaggautawa zuwa cikarsa,
Ba zai zama ƙarya ba.
Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri,
Hakika zai zo, ba zai makara ba.